Cutar Pneumonia, amai da gudawa da zazzabin cizon sauro sun fi kashe kananan yara a Afirka

Cutar Pneumonia, amai da gudawa da zazzabin cizon sauro sun fi kashe kananan yara a Afirka

Babban daraktan kamfanin Novartis, Vas Narasimhan, ya bayyana Pneumonia, zazzabin cizon sauro da gudawa a matsayin manyan cututtuka uku da suka fi kashe yara a Afirka.

Narasimhan wanda shi ne shugaban kamfanin hada magunguna na Novartis ya bayyana hakan ne a ranar Talata cikin sakon sa na Ranar Yaran Afirka ta bana.

Ya yi kira ga shugabannin Afirka da su dauki matakin kare kananan yara daga wadannan cututtukan.

A cewar Narasimhan, ana iya samun mace-macen kananan yara sau takwas a Afirka wadanda basu haura shekaru biyar ba a duniya gabanin a samu mutuwar guda a nahiyar Turai.

Ya ce cutar sanyi dake kama hakarkari wato ‘Pneumonia’, ta fi kowace cutar saurin kashe kananan yara a duniya.

Cutar Pneumonia, amai da gudawa da zazzabin cizon sauro sun fi kashe kananan yara a Afirka
Cutar Pneumonia, amai da gudawa da zazzabin cizon sauro sun fi kashe kananan yara a Afirka
Asali: Twitter

Ya ce, “a kowane sakan 39, cutar Pneumonia ta na kashe yaro daya a duniya. Wannan cuta da za a iya hana kamuwa da ita tana kashe yara fiye da kowace cuta a Afirka da duniya duniya baki daya."

“Cutar Pneumonia, amai da gudawa, da zazzabin cizon sauro su ne manyan cututtuka uku da ke kashe ƙananan yara a Afirka, inda ake samu mutuwar akalla yara miliyan ɗaya duk shekara."

"Hakanan ciwon sikila, ita kadai ce cutar da ake gadonta da ta fi kowace cuta kassara kananan yara a fadin duniya, kuma ta fi yi wa 'yan Afrika illa."

"Cutar sikila ta na kara saurin kamuwa da wasu cututtukan musamman cutar zazzabin cizon saura da kuma Pneumonia."

KARANTA KUMA: Shugaban jam'iyyar APC ya mutu a kasar Afrika ta Kudu

Narasimhan ya bayyana damuwa dangane da yadda kananan yara 300,000 'yan kasa da shekaru biyar suke mutuwa duk shekara a dalilin amai da gudawa duk da ana samun maganin cutar cikin sauki.

Dangane da cutar zazzabi cizon sauro, ya ce "yaki da zazzabin cizon sauro na daya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a bangaren kiwon lafiya."

"Daga shekarar 2000 zuwa 2015, yawan mace-macen kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar ya ragu da fiye da kashi 70 cikin dari a Afirka."

"Sai dai har yanzu muguwar cutar tana kashe sama da kananan yara 270,000 ‘yan kasa da shekaru biyar duk shekara."

"A yau muna kira ga mahukuntan lafiya na duniya da su ci gaba da amfani da karfin ikonsu wajen tattara albarkatu domin tabbatar da cewa dukkan yara zasu iya girma ba tare da kamuwa da cutar Pneumonia, amai da gudawa ko kuma zazzabin cizon sauro."

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, a kowace shekara a ranar 16 ga Yuni, kungiyar kasashen Afirka da sauran mambobinta suna bikin tunawa da ranar Yaran Afrika.

Ana bikin wannan rana domin tunawa da ranar 16 ga Yunin 1976, inda a birnin Soweto na kasar Afirka ta Kudu, aka yi wa ɗaliban da suka yi zanga-zangar nuna adawa da ilimin wariyar launin fata kisan gilla.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng