Shugaban jam'iyyar APC na kasar Afrika ta Kudu ya mutu
- Mun samu rahoton cewa mai yankan kauna ta katse hanzarin daya daga cikin shugabannin jam'iyyar APC
- Dr. Taiye Olusola Abe, shugaban jam'iyyar APC na kasar Afrika ta Kudu ya bar duniya yana da shekaru 65
- Babban mashawarci na musamman kan harkokin sadarwa ga shugaba Buhari, Femi Adesina, shi ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a kan shafinsa na Facebook
- Shugaban kasa Buhari ya yi alhinin mutuwar Dr. Olusola, inda ya bai wa 'yan uwansa da makusansa hakurin rashin da suka yi
Jam'iyya mai mulki a Najeriya APC, ta fada cikin zulumi yayin da ta yi rashin daya daga cikin shugabanninta a kasar Afrika ta Kudu, Dr. Taiye Olusola Abe.
Rahoton mutuwar Dr.Olusola ta jefa shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin yanayi na damuwa da bakin ciki.
Mun samu rahoton cewa, mai yankan kauna ta katse hanzarin Marigayi Olusola yayin da ya bar duniya yana da shekaru 65.
A yayin tattaro wannan rahoto da jaridar Legit.ng ta yi, ba a iya gano musabbabin mutuwar shugaban jam'iyyar ba.

Asali: Twitter
Da ya ke martani dangane da mutuwar shugaban jam'iyyar ta su, shugaba Buhari ya yi alhini tare da mika sakon ta'aziyarsa zuwa ga 'yan uwa, abokanai da makusantan marigayin.
Sanarwar hakan tana kunshe cikin sakon da mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina ya wallafa kan shafinsa na sada zumunta a ranar Laraba, 17 ga watan Yuni.
KARANTA KUMA: Sarkin Daura, Umar Farouk, ya sauya fasalin majalisar hakimai
A sakon gaisuwa gami da nuna alhini, shugaba Buhari ya nemi iyalai da makusantan marigayi Abe da su dauke dangana. Ya kuma yi addu'ar neman Ubangiji ya ba su hakuri da juriyar rashin.
Ya misalta marigayi Abe a matsayin mutum wanda ba ya da shakkun soyayyar da ya ke yi wa Najeriya. Ya ce marigayin Abe mutum ne wanda ya sadaukar da kansa ga akidun jam’iyyar APC.
Haka kuma shugaban kasa Buhari ya hikaito irin kusancin da ya samu yayin ganawa karo daban-daban da suka rika yi da Marigayi Abe a lokuta mabanbanta da ya ziyarci kasar Afrika ta Kudu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng