Bashin da ake bin Najeriya: Lai Mohammed ya yi wa Atiku martani mai zafi

Bashin da ake bin Najeriya: Lai Mohammed ya yi wa Atiku martani mai zafi

Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu na Najeriya, ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na yada zantukan karya kuma masu tsoratarwa game da yawan bashin da ake bin Najeriya.

Kamar yadda tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana, kamar yadda MTEF da FSP suka nuna, yawan bashin da ake bin Najeriya da kuma kudin shigarta ya kai kashi 99 a watanni uku na farkon 2019.

Amma a takardar da Mohammed ya fitar a ranar Laraba, 17 ga watan Yuni, ya ce babu kamshin gaskiya a zancen Atiku ko kadan.

"Babu shakka tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yana kaunar kasar mu kuma yana mana fatan alheri. Idan ba haka ba, ba zai ci gaba da fatan zama shugaban kasa ba," ministan yace.

Bashin da ake bin Najeriya: Lai Mohammed ya yi wa Atiku martani mai zafi
Bashin da ake bin Najeriya: Lai Mohammed ya yi wa Atiku martani mai zafi Hoto: The Cable
Asali: Facebook

"Muna fatan kalaman da yake amfani da su a kan irin lalacewar tattalin basu nufin wani abu daban da ya wuce kaunar kasar nan a wannan lokacin.

"Har a halin yanzu, mun kasa gano inda ya samo N943.12 biliyan na bashi da kuma N950.56 biliyan na kudin shiga a watanni uku na farkon 2020 da yake magana a kai."

Mohammed ya ce ba wai kuskure kadai Atiku yayi a kan maganar bashi ko kudin shiga ba, kwata-kwata babu gaskiya a al'amarin.

"Abinda yasa bashi ya hauhawa kuma kudin shiga yayi kasa a Najeriya shine yadda muka dogara da sashin man fetur," yace.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya na ranto kudi ne saboda ayyukan more rayuwa na kasar nan.

"Babu shakka, a duk inda aka samu tabarbarewar kayayyakin more rayuwa, babu gwamnatin da za ta tankwashe kafa ta kalla ba tare da yin wani abu a kai ba," yace.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Zan shirya taron majalisar zartarwa na ba da dadewa - Sabon shugaban APC ya yi tsokaci

"Bashin da aka karbo don bangaren ilimi zai taka rawar gani wurin gina 'yan kasa yayin da na bangaren noma da kiwo zai fadada tattalin arziki."

A watan Disamban 2019, yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai N27.4 tiriliyan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel