Ban sauya sheka ba duk da na bar APC - Obaseki

Ban sauya sheka ba duk da na bar APC - Obaseki

Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo, ya ce har yanzu bai koma wata jam'iyyar siyasa ba. Gwamnan ya sanar da barin jam'iyyar APC bayan ya gana da Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata.

Ya ce zai ci gaba da neman zarcewarsa a wata jam'iyya.

Amma kuma, bayan gwamnan ya sanar da barin jam'iyyar APC, kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin babbar kotun tarayya ta dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.

Ajibola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo ya bayyana a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar APC na kasa.

A wata wallafa da Obaseki ya yi sa'o'i kadan bayan tabbatar da dakatar da Oshiomhole, Obaseki ya ce har yanzu bai koma wata jam'iyya ba, amma ya mayar da hankali wurin yakar COVId-19 a jihar.

An hana Obaseki tsayawa takara a karkashin jam'iyyar APC bayan tantance 'yan takara da aka yi.

Akwai hasashen da ke nuna cewa akwai yuwuwar komawarsa jam'iyyar PDP. Ya samu damar ganawa da wasu gwamnoni da aka zaba karkashin jam'iyyar PDP a ranakun karshen mako.

Har yanzu dai ba a san ko zai koma jam'iyyar APC ba bayan dakatar da Oshiomhole da aka yi a matsayin shugaban APC.

Amma kuma gwamnonin APC sun tabbatar da cewa za su tabbatar da an bi damokaradiyyar cikin gida yayin zaben dan takara a zaben ranar 19 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Ba zan iya da jarabarsa ba, tsawon dare babu sassauci - Matar aure mai neman saki

A jiya Legit.ng ta ruwaito cewa, kotun daukaka kara da ke Abuja ta jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A ranar 4 ga watan Maris ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar wasu mambobin APC shida na jihar Edo wajen dakatar da Oshiomhole.

Alkalan kotun da suka samu jagorancin shugaban alkalan kotun daukaka kara, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta yanke hukuncin cewa daukaka karar dakatar da Oshiomhole bata da tushe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel