Oshiomole ya sayar da jam'iyyarmu, mara alkawari ne - Shugaban kungiyar gwamnonin APC

Oshiomole ya sayar da jam'iyyarmu, mara alkawari ne - Shugaban kungiyar gwamnonin APC

Dirakta janar na kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Salihu Lukman, ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomole, ya sayar da rayuwar jam'iyyar ga wasu wadanda ke kokarin ganin bayanta.

Hakan ya biyo bayan hukuncin kotun daukaka karar da ta tabbatar da dakatad da Adams Oshiomole matsayin shugaban jam'iyyar.

A jawabin da ya saki, Lukman ya ce maganar gaskiya itace jam'iyyar APC ta fara fita daga hayacinta na demokradiyya da ya kamata ta baiwa kowa hakkin takarar zabe.

Ya ce idan akayi waiwaye kan irin faduwar da jam'iyyar ta samu a zaben 2019, ya kamata kowani dan jam'iyyar APC ya damu.

Oshiomole ya sayar da jam'iyyarmu, mara alkawari ne - Shugaban kungiyar gwamnonin APC
Salihu Lukman
Asali: Facebook

Yace: "Abin da ke faruwa a APC ya fara saba hankali. Maganar gaskiya ita ce an fara jefa jam'iyyar cikin wani hali da ya saba ka'idojin demokradiyya na baiwa kowa daman takara."

"Ya kamata a ce wasu sun dau matakin shawo kan lamarin, amma da alamun ana son maimaita abubuwan takaicin da suka faru a baya a lokutan da ake shirin zabe."

"Anyi a jihar Ribas, Zamfara da Bayelsa. Yanzu kuma jihar Edo da Ondo na kan hanyar fuskantar matsaloli irin wanda ya janyo mana fadi a na Zamfara da Bayelsa. Saboda me zamu bari hakan ya faru?"

"Ya bayyana karara cewa shugabancin jam'iyyar karkashin jagorancin kwamred Adams Oshiomole malalaciya ce kuma shi bai cancanci bashi amanan shugabantar jam'iyyar ba."

KU KARANTA: Dalilin da yasa muka fasa bude Masallatai da Majami'u - Gwamnan jihar Legas

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Kotun daukaka kara da ke Abuja ta jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Zaku tuna cewa a ranar 4 ga watan Maris ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar wasu mambobin APC shida na jihar Edo wajen dakatar da Oshiomhole.

Alkalan da suka samu jagorancin shugaban alkalan kotun daukaka kara, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta yanke hukuncin cewa daukaka karar dakatar da Oshiomhole bata da tushe.

Wannan hukuncin na zuwa ne a ranar da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya fita daga jam'iyyar APC bayan ganawarsa da Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel