Katsina: Buhari ya aika sako ga masu zanga - zanga a kan rashin tsaro

Katsina: Buhari ya aika sako ga masu zanga - zanga a kan rashin tsaro

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya roki mutanen jihar Katsina su kara hakuri tare da bawa gwamnatinsa hadin kai da goyon baya a kokarinta na tabbatar da an samun zaman lafiya a jihar.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata.

A cikin jawabin, shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya da jaje ga wadanda suka yi asarar makusanta da dukiya sakamakon hare - haren 'yan bindiga.

A cewar shugaba Buhari, rundunonin tsaro na kasa za su iya shawo kan kalubalen tsaron da 'yan bindiga da 'yan ta'adda suka jefa kasa a ciki.

Shugaba Buhari ya yi gargadin cewa mamaye tituna da sunan zanga - zanga zai iya kawo tsaiko ga aikin rundunar soji na murkushe 'yan bindiga a jihar Katsina.

Kazalika, ya yi kira ga mutanen jihar Katsina da su bawa sojoji hadin kai domin za su kawo karshen 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci a cikin kankanin lokaci.

Katsina: Buhari ya aika sako ga masu zanga - zanga a kan rashin tsaro
Buhari
Asali: Twitter

"An gano cewa wadannan 'yan bindiga suna buya ne a jeji mafi girma a yankin arewa maso yamma. Atisayen rundunar soji zai kawo karshen zamansu a cikin jejin," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Shekau ya saki sabon bidiyo, ya nemi 'yan bindiga su hada kai da Boko Haram

Shugaban kasa ya nemi karin hakuri daga wurin jama'a yayin da sojoji ke dauka matakan da suka dace domin tabbatar da dawowar zaman lafiya a jihar Katsina da sauran sassan Najeriya.

A ranar Talata ne dumbin jama'a a jihar Katsina suka mamaye manyan tituna a jihar domin nuna fushinsu tare da aika sako ga gwamnati a kan halin rashin tsaro da suke ciki.

Dumbin fusatattun masu zanga - zangar sun ce 'yan bindiga suna hallaka mutane 20 zuwa 100 a kowacce rana.

Masu zanga - zangar sun mamaye kofar shiga gidan gwamnatin jihar Katsina tare da neman gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya yi murabus tunda ya amsa cewa ya gaza kare rayuka da dukiyar jama'ar da suka zabe shi.

A ranar Litinin ne gwamna Masari ya fito ya shaidawa duniya ya gaza kare jama'arsa daga hare -0 haren 'yan bindiga, wanda ya zama ruwan dare a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel