Ganduje zai zaftare kashi 30% a kasafin kudin Kano na bana

Ganduje zai zaftare kashi 30% a kasafin kudin Kano na bana

Gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar shirin da ta ke yi na rage kasafin kudin jihar da kaso 30 cikin 100.

Kamar dai yadda ta kasance ga gwamnatin tarayya, gwamnatin Kano ta kudiri aniyar zaftare kasafin kudin jihar na bana sakamakon karayar tattalin arziki da annobar korona ta haddasa.

Babu shakka ragin da gwamnatin Kano za ta yi a kasafin kudin jihar ya samo asali ne sakamakon matsalar tattalin arzikin da annobar korona ta haifar a duniya baki daya.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yayin da ya ke jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar cikin fadarsa a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni.

An shirya taron ne a wani bangare daga shagulgulan murnar zagayowar ranar dimokuradiya ta wannan shekara da aka gudanar tun a ranar Juma'a 12 ga watan Yuni.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje
Hakkin Mallakar Hoto: Fadar Gwamnatin Kano
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje Hakkin Mallakar Hoto: Fadar Gwamnatin Kano
Asali: UGC

A cewar Ganduje, saboda kalubalen da ake fuskanta wanda annobar korona ta haifar, za a yi dogon nazari gami da bita kan kasafin kudin jihar na bana domin zaftare wani kaso daga cikinsa.

Daga bisa kuma za a mika kasafin kudin zuwa majalisar dokokin jihar domin ta yi nata nazari da kuma amincewa ta hanyar sanya shi cikin doka.

KARANTA KUMA: Hukumar JAMB ta kayyade makin shiga jami'a da sauran makarantu na gaba da sakandire

Ya kara da cewa, za a yi iyaka bakin kokari wajen ganin cewa kasafin kudi da za a yiwa kwaskwarima, ba zai kawo tangarda ba a bangaren tsaro, kiwon lafiya da kuma ilimi a jihar ba.

"Za mu dage don ganin cewa kwaskwarimar da za a yi wa kasafin kudin na bana ba ta shafi bangaren tsaro, kiwon lafiya, ilimi da kuma sauran muhimman bangarori na gwamnati ba."

"Muna sake yin nazari a kan kasafin kudin jihar inda za mu rage kashi 30 cikin 100, domin ya daidaita da kalubalan wannan annoba ta cutar COVID-19."

"Kuma nan ba da jimawa za a kai shi Majalisar Dokokin Jihar domin ta sauke nauyin da rataya wuyanta wajen shigar da shi cikin doka," inji gwamnan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel