Ciyar da 'yan makaranta: Majalisar wakilai ta caccaki FG a kan kashe N187bn

Ciyar da 'yan makaranta: Majalisar wakilai ta caccaki FG a kan kashe N187bn

Majalisar wakilan Najeriya ta soki gwamnatin tarayya a kan ikirarin kashe N187 biliyan a kan ciyar da 'yan makaranta.

Kwamitin majalisar da ke kula da baitul Mali ta ga rashin dacewar hakan tare da caccakar shugabar shirin ciyarwar, Temitope Sinkaye.

Shugaban kwamitin, Oluwole Oke, ya kwatanta al'amarin da mara dadi kuma abinda ba zasu lamunta ba.

A saboda haka, kwamitin ta bukaci bayanin yadda shirin ya kashe kudin dalla-dalla.

'Yan majalisar sun matukar fusata da takardun da kwamitin ya bada wanda NICTO ta samu bashin $400 miliyan daga bankin duniya, $321 miliyan daga kudaden Abacha da kuma wata $400 miliyan daga gwamnatin tarayya.

Sikanye ya sanar da kwamitin cewa shirin ciyarwar ya fara tun daga 2016 lokacin da ma'aikatar walwala da jin kan dan kasa ta kirkiro shi kuma ya lamushe N186 biliyan.

Ta ce an kashe N63.2 biliyan a 2018, N32.2 biliyan a 2019 da kuma N124.4 biliyan a 2020.

Ciyar da 'yan makaranta: Majalisar wakilai ta caccaki FG a kan kashe N187bn
Ciyar da 'yan makaranta: Majalisar wakilai ta caccaki FG a kan kashe N187bn. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: FG ta lissafa sharruda 6 na bude makarantu

Mambobin kwamitin sun musanta wannan lissafin saboda hatta mazabunsu basu san da shirin ba.

Ifeanyi Momah daga jihar Anambra karkashin jam'iyyar APGA da Miriam Onuoha daga jihar Imo a karkashin jam'iyyar APC sun yi watsi da wannan rahoton.

Momah ya musanta ikirarin da aka yi na cewa dalibai 200,000 ne suka mora ciyarwar daga karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra inda yake wakilta.

Oke ya ce kwamitin zai duba takardun da aka gabatar amma ya nuna tantamarsa idan majalisar dattawa ce ta fitar da kudin.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da sharrudan bude makarantun sakandare da na gaba da sakandare a kasar.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya bayar da sanarwar sharrudan a ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

Ya yi wannan jawabin ne a taron tsare tsare na 2020 a kan matakin daukan dalibai a makarantun gaba da sakandare da hukumar JAMB za ta yi.

Kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito, ministan ya yada wa makarantun gaba da sakandare a Najeriya kan matakan da suka dauka na bayar da gudunmuwa wurin yaki da annobar ta korona.

Amma ministan ya yi gargadin cewa kada makarantun su bude ba tare da samun izini daga wurin gwamnatin tarayya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel