JAMB ta kayyade makin shiga jami'a da sauran makarantu na gaba da sakandire

JAMB ta kayyade makin shiga jami'a da sauran makarantu na gaba da sakandire

Hukumar shirya jarabawar shiga Jami’a da wasu makarantu na gaba da sakandire JAMB, ta kayyade yawan makin da sai dalibai sun samu kafin samun nasarar ci gaba da karatunsu.

Hukumar JAMB ta amince da 160 a matsayin maki mafi karanci don samun gurbin karatu a jami'oin gwamnati da ke fadin tarayya kasar nan a bana.

An kayyade wannan maki a yayin taron tsara hanyoyin shiga makarantun gaba da sakandire karo na 20 da ta gudanar a ranar Talata.

Taron wanda aka gudanar da shi ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna, hukumar ta kuma kayyade 140 a matsayin mafi karancin makin samun damar shiga jami'o'i masu zaman kansu.

Haka kuma hukumar JAMB ta kayyade 120 a matsayin mafi karancin makin shiga makarantun polytechnic na gwamnati. Sai kuma 100 na kwalejin ilimi da makarantun koyon sana'a.

Shugaban JAMB; Ishaq Oloyede
Hakkin mallakar hoto; Jaridar Punch
Shugaban JAMB; Ishaq Oloyede Hakkin mallakar hoto; Jaridar Punch
Asali: UGC

Yayin taron wanda shugaban Hukumar JAMB na kasa, Ishaq Oloyede ya jagoranta, ya nemi dukkanin makarantun gaba da sakandire a kan kada kudin tantance dalibai ya haura naira 2000.

Sai dai kamar yadda aka saba, har yanzu jami’o’i na da damar kara yawan makin ga dalibai fiye da adadin da hukumar JAMB ta kayyade.

Oloyede ya bayyana cewa, jami'oi da makarantun gaba da sakandire sun bai wa dalibai 612,557 damar ci gaba da karatunsu cikin dalibai 1,157,977 da suka zana jarabawar JAMB a bara.

Da ya ke ci gaba da gabatar da jawabai, Oloyede ya nemi makarantun gaba da sakandire su ci gaba da aiwatar da shirin daukan dalibai a bana bisa ka'idojin da aka amince dasu.

KARANTA KUMA: Atiku ya sake caccakar gwamnatin Buhari a kan dorawa Najeriya nauyin bashi

Hukumar ta sanar da wannan mataki bayan kammala babban taro na masu ruwa da tsaki kan sha’anin ilimi a Najeriya wanda ministan ilimi Adama Adamu ya halarta.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa, Chukwuemeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi shi ne wakilci Adamu Adamu a taron da aka gudanar.

Ministan ya nemi hukumar JAMB da ta yi la'akari da daliban da su gabatar da kyakkyawan sakamako ko da shaidar su ta kammala karantun sakandire (SSCE) ba ta bana bace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel