Shekau ya saki sabon bidiyo, ya nemi 'yan bindiga su hada kai da Boko Haram

Shekau ya saki sabon bidiyo, ya nemi 'yan bindiga su hada kai da Boko Haram

Shugaban kungiyar 'Jama'atu Ahlussunnah Lidda'awati Wal Jihad' wacce aka fi sani da Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon faifan bidiyo a daren ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, 2020.

A cikin sabon bidiyon, Shekau ya nemi 'yan bindigar yankin arewa maso yamma da na yankin arewa ta tsakiya su hada kai da kungiyar Boko Haram.

A cewar jaridar HumAngle, a cikin sabon faifan bidiyon, mai tsawon minti 13 da dakika 49, mutane hudu sun yi magana a cikin harshen Turanci, Fulfulde, Hausa da Faransanci domin aika sako ga jama'ar jihohin Zamfara da Neja.

Dukkan masu maganar sun bukaci mazauna jihohin Zamfara da Neja a kan su tashi tsaye wajen kare hakkin Allah.

"Ya 'yan uwana da ke yankin tekun Chad, da na kasar Kamaru, da na cikin dajin Sambisa, da na jihar Neja da jihar Zamfara; ina kira da baku karfin gwuiwa a kan mu tashi tsaye domin yin aiki saboda Allah," a cewar wani mai magana da aka rufe fuskarsa..

"Duk abinda muke yi, muna yi ne saboda Allah, a saboda haka ina baku karfin gwuiwa ku cigaba. Ku kara dagewa, saboda a cikin Qur'ani, Allah ya bukaci mu kasance masu juriya yayin kare hakkinsa

"Ana ganin muna aikata kisa, muna barna. Allah ne ya bamu umarnin mu kashe duk wanda baiyi imani ba," a cewarsa.

Shekau ya saki sabon bidiyo, ya nemi 'yan bindiga su hada kai da Boko Haram
Shekau ya saki sabon bidiyo, ya nemi 'yan bindiga su hada kai da Boko Haram
Asali: Twitter

Malaman addini da suka saba da hanyoyin da Boko Haram ke farautar sabbin mayaka sun bayyana cewa kungiyar ta yi amfani da harsuna da dama wajen aika sakon ne domin samun mambobi daga sassa daban - daban a cikin Najeriya da kasashen yankin Sahel.

"Mu na aika sako zuwa ga 'yan uwanmu da ke yankin tekun Chad, Kamaru da Sambisa. Mu na aika wannan sako ga 'yan uwa da ke jihohin Neja da Zamfara.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda sun kaiwa sojoji hari, sun kashe 24

"Mu na baku tabbacin cewa mu na cikin koshin lafiya, kuma mu na fatan kuna nan lafiya. Mu na godiya ga Ubangiji da ya doramu a kan wannan hanya, a wannan lokaci, domin kare kalmominsa da kafa shari'arsa.

"Sakona biyu shine zuwa ga jama'ar Najeriya, Kamaru da sauran sassan duniya. Mu na kira da ku zo mu hada kai domin kafa shari'a a fadin duniya.

"Idan ku ka amsa kira, za mu rungumeku hannu bi-biyu bisa tsarin shari'ah, sannan za mu bautawa Allah kamar yadda ya umarce mu," a cewar wani daga cikin masu magana a faifan bidiyon.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel