Rotimi Akeredolu ya ziyarci Buhari da fom dinsa na takarar gwamna

Rotimi Akeredolu ya ziyarci Buhari da fom dinsa na takarar gwamna

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa, Villa, da ke Asorock a birnin tarayya, Abuja.

Akeredolu, mai neman takarar kujerar gwamnan jihar Ondo a karo na biyu a karkashin tutar jam'iyyar APC, ya ziyarci Buhari da fom dinsa na takara.

Jim kadan bayan kammala ganawarsu, Akeredolu ya shaidawa manema labarai cewa shugaba Buhari ya tabbatar masa da cewa yana goyon bayansa.

Ziyarar Akeredolu na zuwa ne jim kadan bayan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sanar da yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar APC bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Obaseki ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban a ranar Talata, 16 ga watan Yuni.

Gwamnan ya yi furucin hakan ne a kan hanyarsa ta fita daga fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Rotimi Akeredolu ya ziyarci Buhari da fom dinsa na takarar gwamna
Rotimi Akeredolu ya ziyarci Buhari
Asali: Twitter

Yayin zantawarsa da manema labarai a fadar, Obaseki ya ce zai nemi takarar zango na biyu a wata jam'iyar ta daban.

Biyo bayan hana shi takara da uwar jam'iyar APC ta yi a ranar Juma'ar da ta gabata, Obaseki ya bayyana cewa zai yanke shawarar matakinsa na gaba bayan ya gana da Buhari.

Shugaban kwamitin tantance 'yan takara na jam'iyyar APC, Jonathan Ayuba, shi ne ya bayar da sanarwar haramtawa Gwamna Obaseki tsayawa takara tun gabanin zaben fidda gwani.

DUBA WANNAN: Ganduje ya goyi bayan APC a kan korar takarar Obaseki, ya yi magana a kan zaben Edo

Ayuba ya bayyana cewa an haramta wa Obaseki tsayawa takara ne sakamakon matsalar da aka gano akwai a tattare da takardunsa na makaranta.

Akwai yiwuwar babu inda gwamna Obaseki zai jarraba sa'arsa ta tsayawa takarar gwamnan sai a karkashin inuwar jam'iyyar PDP bayan ya cika bujensa da iska daga jam'iyyar APC.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa, tuni jam'iyyar PDP ta fara zawarcin gwamna Obaseki yayin da uwar jam'iyyar APC ta huro masa wuta.

An dade ba a ga maciji tsakanin Gwamna Obaseki da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, wanda ya goyi bayansa a shekarar 2016.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel