Da dumi-dumi: Jami'an NCDC sun fitittiki dalibai yayinda suka koma makaranta yau

Da dumi-dumi: Jami'an NCDC sun fitittiki dalibai yayinda suka koma makaranta yau

Jami'an hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC sun fitittiki daliban makarantar West African People’s Institute (WAPI) da suka isa makaranta domin shiga aji.

Hakan ya faru ne da safiyar yau Talata, 16 ga Yuni, 2020 a jihar Cross River. Daily Trust ta ruwaito.

Za ku tuna cewa gwamnan jihar CrossRiver, Farfesa Ben Ayade, a makon da ya gabata ya bada umurnin bude makarantu uku a fadin jihar.

Sauran makarantu biyun sune makarantar sakandaren gwamnati Egola, da kuma makarantar sakandaren gwamnati Ikom.

Daliban yanzu na wajen makarantar WAPI a Calabar.

Jihar Cross River ce jihar daya tilo da ba'a samu bullar cutar Coronavirus ba har yanzu.

Ku saurari cikakken rahoton.....

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel