Najeriya ta kara yin rashin babban farfesa
Allah ya yi wa farfesa Oladipo Akinkugbe rasuwa. Akinkugbe farfesa ne masanin lafiya a asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan, ya rasu a babban birnin jihar a ranar Litinin yayin da yake da shekaru 86 da haihuwa.
Ya karantar tare da koyarwa a manyan jami'o'in duniya. Sun hada da jami'ar London, kwalejin Balliol, jami'ar Oxford da ke Ingila da kuma makarantar horar da likitoci ta Harvard da ke Boston a Amurka.
Shine shugaban Vesta Healthcare Partners kuma shugaban kwamitin tabbatar da ayyuka na fadar shugaban kasa a kan gyaran asibitocin koyarwa da ke fadin Najeriya.
Shine shugaban kwamitin zartarwa na asibitin jami'ar koyarwa da ke Ibadan, Najeriya.
A wani lokaci da ya shude, ya taba zama shugaban hukumar jarabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya (JAMB).
Yayi aiki a matsayin shugaban majalisar zartarwa ta jami'ar Fatakwal, tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, tsohon shugaban jami'ar Ilorin da kuma shugaban sashen likitanci na jami'ar jihar Ibadan.
Ya kwashe shekaru 60 yana aiki kafin yayi murabus.
A wannan lokacin, ya jagoranci bude wuraren duba marasa lafiya na musamman, daya na masu hawan jini dayan kuwa na masu ciwon koda. Sune na farko a Afrika
Bayan yin murabus dinsa, Akinkugbe ya kafa dakin shan maganinsa na masu hawan jini kadai wanda ya kwashe shekaru 20 yana aiki.
Majiyar da ta sanar da mutuwarsa ga jaridar The Nation ta ce ya rasu ne a gidansa da ke Ibadan.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dakarun soji sun harbe kwamandan Boko Haram, Abu Imrana
A wani labari na daban, daya daga cikin manyan 'yan kasuwar man fetur din Najeriya, Anthony Enukeme ya rasu. Ya rasu yana da shekaru 75 a duniya.
Mamallakin kamfanin Tonimas Oil and gas group ya rasu a daren Litinin bayan gajeriyar rashin lafiya.
Wata majiya daga iyalansa wacce ta zanta da jaridar The Nation, ta ce ya mutu ne sakamakon hana zirga-zirgar da aka yi saboda annobar korona.
Ya ce mamacin ya cika shekaru 75 cif a duniya a watan Janairun da ta gabata. Ya saba fita kasar ketare don duba lafiyarsa a kowacce shekara amma sai wannan annobar ta hana.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng