'Na gaza bawa Katsinawa kariya' – Masari

'Na gaza bawa Katsinawa kariya' – Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce ya gaza sauke nauyin da ke kansa na kare Katsinawa daga sharrin 'yan bindiga.

Da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a Katsina, Masari ya ce yana bakin ciki saboda tun hawarsa mulki Katsinawa ba su runtsa ba.

Ya ce gara dabobi da yan bindigan domin su kashe mutane barkatai suke yi babu dalili kamar yadda The Cable ta ruwaito.

'Na gaza bawa Katsinawa kariya' – Masari
'Na gaza bawa Katsinawa kariya' – Masari. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna)

"Ban san abinda zan fada musu ba. Ba zan iya kallon kwayoyin idanunsu ba domin mun gaza kare su akasin alkawarin da muka dauka na kare rayuka da dukiyoyinsu a jihar," in ji gwamnan.

"Ban taba tsamanin yan bindigan da ke zaune a daji za su aikata haka ba, halin da suke nuna wa yafi na dabobi muni.

"A daji, zaki ko damisa kan kashe dabba ne kawai idan yana jin yunwa kuma ba dukka dabobi ya ke kashe wa ba, wanda zai ci kawai ya ke kashe wa a lokaci guda.

"Amma abinda muke gani shine yan bindiga za su shigo gari, suyi ta ruwan harsashi suna kashe mutane ba dalili, kamar kisar da aka yi baya bayan nan a Faskari da wasu sassan karamar hukumar Dandume.

"Ta yaya mutum zai rika aikata abinda ko dabba ba zai aikata ba?”

Babu wasu mutane masu gaskiya a daji.

"Aikin mu shine tallafawa hukumomin tsaro wadda na ke ganin muna yi fiye da kashi 90 cikin 100 bisa la'akari da kudaden da muke da shi," in ji shi.

Wannan kalaman na Masari na zuwa ne bayan Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi ikirarin cewa Shugaba Buhari da gwamnonin Arewa sun gaza wurin samar wa mutanensu tsaro.

Gwamnatin Masari ta janye daga sulhun da ta kulla da yan bindiga bayan an cigaba da samun hare hare a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel