Yanzu-yanzu: Ganduje ya bada umarnin ci gaa da bincikar Sarki Sanusi II

Yanzu-yanzu: Ganduje ya bada umarnin ci gaa da bincikar Sarki Sanusi II

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bai wa hukumar sauraron koke da yaki da rashawa ta jihar Kano da ta ci gaba da bincike a kan tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

A makon da ya gabata ne wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Litinin ta kori karar da tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, wacce ke bukatar dakatar da bincikar zargin wata almundahanar filaye da masarautar jihar Kano ta yi.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, a ranar 6 ga watan Maris din 2020 ne tsohon basaraken ya tunkari kotun da bukatar cewa a dakatar da Ganduje, antoni janar da kuma shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar a kan bincikarsa.

Korafin ya bukaci kotun da ta dakatar da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano da shugabanta, Muhyi Rimingado, da ya dakata da bincikarsa har sai an kammala shari'ar farko.

Alkali mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ya yanke hukuncin cewa, hukumar ba ta take wani hakki na tsohon basaraken ba na bincikarsa a kan zargin da ake masa.

Daga nan Allagoa ya yi watsi da karar, tare da tabbatar da cewa babu wani hakkin na Sanusin da aka yi wa karantsaye.

KU KARANTA: Tattalin arziki: Sanusi II ya yi muhimmin kira ga gwamnatin tarayya, ya yi gagarumin hasashe

A yayin sanar da sakamakon zaman kotun, Abubakar Ibrahim, babban mataimaki na musamman ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, "Babban kotun tarayyar karkashin mai shari'a Allagoa ya yi watsi da bukatar tsohon sarkin Kanon a kan PCACC.

"A hukuncin da ya yanke a yau Litinin, 8 ga watan Yuni, kotun ta bai wa hukumar yaki da rashawa da ta ci gaba da bincikar tubabben sarkin."

Karin bayani na tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel