Ana wata ga wata: Likitoci sun tsunduma yajin aiki
Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki (NARD) sun sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani bayan karewar wa'adin mako biyu da suka bawa gwamnatin tarayya.
Da ya ke sanar da hakan yayin wani taro da manema labarai ranar Litinin, shugaban kungiyar NARD, Aliyu Sokomba, ya ce sun yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan wani taro da suka gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo a ranar Lahadi.
Sokomba ya bayyana cewa yajin aikin bai shafi sauran mambobin kungiyar NARD da ke aiki a cibiyoyin masu kula da cutar korona ba.
Sai dai, ya bayyana cewa matukar babu abinda ya sauya bayan sati biyu, zasu umarci likitocin su shiga yajin aiki.
Ya kara da cewa sun yafewa likitocin shiga yajin aikin a wannan lokacin saboda saka bakin da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi.
Shugaban majalisar wakilai da shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan harkar lafiya da sauran masu ruwa da tsaki sun yi kokarin kawo sulhu a tsakanin likitocin da gwamnatin tarayya.
Sokomba ya bukaci 'yan Najeriya su yi hakuri, su fahimci dalilinsu na shiga yajin aiki a wannan lokaci.
A cewar shugaban, daga dalilansu na shiga yajin aiki akwai bukatar a samar musu da isassun kayan kare kansu (PPE) yayin da suke aikin kulawa da wadanda suka kamu da kwayar cutar korona.
DUBA WANNAN: Maiduguri: Mutum daya ya mutu, da dama sun raunata yayin arangama tsakanin Sojoji da kwamitin yaki da Korona
"Mun bukaci a kaddamar da tsarin biyan hakkokin likitoci masu neman kwarewar aiki kamar yadda ya ke a ko ina a fadin duniya. A samar da kudaden bawa likitoci horo a cikin kasafin kudin shekarar 2021," a cewar Sokomba.
Sanna ya cigaba da cewa, "a gaggauta kaddamar da fara biyan alawus na musamman saboda hatsarin da ke tattare da aikin likita da kuma fara biyan alawus ga ma'aikatan lafiya da ke kula da ma su cutar korona.
"A dakatar tare da mayar da dukkan kudaden da aka yankewa likitoci daga albashinsu a jihar Kaduna da sauran wasu jihohi."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng