'Na dawo daga rakiyar Buhari, na koma gidan Atiku - Dele Momodu

'Na dawo daga rakiyar Buhari, na koma gidan Atiku - Dele Momodu

Dele Momodu, fitaccen dan jarida da ya taba yin takarar shugaban kasa, ya ce ya zabi ya goyi bayan Atiku a zaben 2019 saboda babu abinda ya ke sauyawa a tattare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A cewar Momodu, gwamnatin shugaba Buhari ta gurgunta 'yancin cin gashin kai na majalisun kasa da bangaren shari'a.

Yayin wata hira da shi a wani shiri mai taken 'Osasu Show', Momodu ya ce jam'iyyar APC ta yaudari masu zabe, ta yaudari sojoji, sannan ba mulkin dimokradiyya ta gaskiya suke yi ba.

"Maganar gaskiya jam'iyyar APC ba ta nuna cewa za ta iya sauya komai ba kamar yadda ta dauki alkawari a shekarar 2015.

"Na yi rubutu daban - daban zuwa shugaban kasa amma duk da haka babu abinda ya sauya, ya zama dole na kara gaba domin na gwada wani mutumin," a cewarsa.

"Jam'iyyar PDP ta tsayar da Atiku a zaben 2019, ya yi rashin sa'ar cin zabe saboda tuni bangaren gwamnati sun gama tsara yadda zasu ci zabe.

"Su ne suke juya hukumar zabe (INEC), sannan sune masu sojoji, har wasan gwaji suka yi a jihar Osun, mun yi korafi tare da sanar da duniya cewa ba dimokradiyya suke yi ba, a cewar Momodu.

Fitaccen dan jaridar ya ce tuni majalisa ta zama tamkar amaryar bangaren zartarwa, yayin da ya ce bangaren shari'a yana fuskantar fyade a hannun bangaren zartarwa.

Kazalika, kungiyar dattijan arewa (NEF) ta koka a kan halin rashin tsaro da arewa ke ciki tare da zargin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da gaza yin maganin matsalar.

A cikin wani jawabi da ya fito ranar Lahadi, jagoran kungiyar, Ango Abdullahi, ya ce lamari rashin tsaro ya na kara tabarbarewa a kullum.

'Na dawo daga rakiyar Buhari, na koma gidan Atiku - Dele Momodu
Buhari da Dele Momodu
Asali: UGC

Ya ce yawaitar hare - haren 'yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram ke kaiwa alama ce da ke nuna cewa gwamnatin Buhari "ta fadi kasa warwas" a bangaren tsaro da walwalar 'yan kasa.

DUBA WANNAN: MC Tagwaye; mai barkwanci ta hanyar kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa (Hotuna)

"Kungiyar dattijan arewa ta damu matuka a kan yawaitar hare - hare da asarar dukiya a yankin arewacin Najeriya.

"Yadda 'yan bindiga suke cin karensu babu babbaka ya nuna cewa yanzu yankin arewacin Najeriya yana hannun 'yan ta'adda, sai yadda suka ga dama suke yi.

"A bayyane take cewa gwamnatin Buhari da gwamnatocin jihohi sun rasa yadda zasu bullowa lamarin, sun gaza kare rantsuwar da suka yi a kan cewa zasu kare jama'a da dukiyoyinsu.

"Lamarin tsaro kullum kara tabarbarewa yake yi saboda 'yan ta'adda sun fahimci cewa akwai raunin shugabanci a wannan gwamnati, lamarin da ya basu karfin gwuiwar kai munanan hare - hare a kan jama'a," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel