Ganduje ya kara rana guda a ranakun sassauta dokar kulle a Kano

Ganduje ya kara rana guda a ranakun sassauta dokar kulle a Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da kara ranar Litinin a cikin jerin kwanakin da ake sassauta dokar kulle a jihar Kano.

Abba Anwar, babban sakataren yada labaran gwamna Ganduje, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

"Domin kara rage wahalhalun da jama'a ke fuskanta sakamakon bullar annobar korona, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da shigar da ranar Litinin a cikin jerin ranakun sassauta dokar kulle a fadin jihar Kano," a cewar anarwar.

A baya gwamnatin jihar Kano ta bawa jama'a damar fita tare da bude kasuwanni a ranakun Lahadi, Laraba da kuma Juma'a.

A cewar sabuwar sanarwar, "kara sassauta dokar kulle a ranar Litinin ya mayar da ranakun janye dokar kulle zuwa ranaku hudu a cikin sati.

"Daga yanzu jama'a zasu iya fita harkokinsu a ranar Litinin, kamar yadda suka saba a sauran kwanaki uku da suka saba, daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma.

Ganduje ya kara rana guda a ranakun sassauta dokar kulle a Kano
Ganduje
Asali: Facebook

"Ina kira ga jama'a da su cigaba da kiyaye dokokin kare yaduwar annobar korona.

DUBA WANNAN: Maiduguri: Mutum daya ya mutu, da dama sun raunata yayin arangama tsakanin Sojoji da kwamitin yaki da Korona

"Jama'a zasu cigaba da saka takunkumin fuska, nesanta da junansu, amfani da sinadrin tsaftace hannu da yawan wanke hannu da sabulu," a cewar ganduje.

Kazalika, gwamna Ganduje ya ce ya zama wajibi kasuwanni da sauran wuraren taron jama'a su cigaba da daukan matakan kiyayewa domin ganin cewa an hana annobar korona samun sukunin yaduwa a tsakanin jama'ar jihar Kano.

(NAN)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel