Dan siyasa ya yi rabon igiyoyi ga mutanen mazabarsa a Arewa (Hotuna)

Dan siyasa ya yi rabon igiyoyi ga mutanen mazabarsa a Arewa (Hotuna)

- Wani dan siyasa mai suna Daniel Ukpera dan asalin jihar Binuwai ya shiga kanun labarai a kan kyautarsa

- Kamar yadda rahoton da aka wallafa a kafar sada zumuntar Facebook ya nuna, ya bai wa jama'arsa igiyoyi don daure akuoyinsu a karamar hukumar makurdi

- Ukpera ya yi bayanin cewa, wannan tallafin nasa zai hana yawon akuyoyi kamar yadda dokar hana kiwon dabbobi a sake ta 2017 ta tanada

Dan siyasa Daniel Ukpera ne ke tashe a kanun labarai tare da kafafen sada zumuntar zamani.

Ukpera dan siyasa ne a jihar Binuwai wanda ya raba igiyoyi ga jama'ar sa don su samu sauki wajen daure akuyoyinsu a karamar hukumar Makurdi ta jihar.

Tsohon dan takarar majalisar jiha na mazabar Guma a 2019, ya yi bayanin cewa ya bada wannan kyautar ne saboda biyayya ga dokar hana yawon dabbobi ta 2017.

A yayin bada gudumawar a Imande Akpu da Tse-Chagu da ke yankin, Ukpera ya ce gwamnatin ta saka dokar yawon dabbobi don haka dole ne su zama madubin dubawa ga 'yan baya.

Ya yi bayanin cewa ya zabi yankunan Tse-Chagu da Imande Akpu ne saboda an gano cewa sune suka fi kowanne yankin yawan awakai a karamar hukumar.

Duk da wayar da kai da aka yi a kan bukatar killace awaki, Ukpera ya dauka sunayen jama'ar da suka bukaci igiyar, amma basu samu ba tare da yi musu alkawarin kawo musu gudumawarsu.

John Tyeku, dattijo da yayi martani a madadin wadanda suka samu gudumawar, ya mika godiyarsa tare da kwatanta lamarin da babban ci gaba.

Dan siyasa ya yi rabon igiyoyi ga mutanen mazabarsa a Arewa (Hotuna)
Dan siyasa ya yi rabon igiyoyi ga mutanen mazabarsa a Arewa (Hotuna)
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Bayan musayar wuta, dakarun soji sun fatattaki 'yan Boko Haram

A wani labari na daban, likitoci a kasar India sun sha mamaki bayan da suka cire cajar waya mai tsawon kafa biyu daga mafitsarar wani mutum mai shekaru 30 bayan fara bude cikinsa da suka yi.

Majinyacin wanda a halin yanzu ake bincikar lafiyar kwakwalwarsa, ya sanar da likitocin cewa ya hadiye cajar ne ta bakinsa amma sai suka gano cewa ta mazakutarsa ta shiga.

Daya daga cikin likitocin da ya yi wa mutumin aiki, Wallie Islam ne ya wallafa labarin a Facebook. Ya ce majinyacin ya dinga korafin ciwon ciki sannan akwai lokacin da ya hadiye amsa kuwwar waya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: