Karar harbi a fadar shugaban kasa: PDP ta yi martani

Karar harbi a fadar shugaban kasa: PDP ta yi martani

- Jam'iyyar PDP ta bukaci a yi bincike a kan harbi da karantsayen tsaro da aka samu a fadar shugaban kasa

- Jam'iyyar ta ce ta shiga matsananciyar damuwa a kan abinda yasa za a yi harbi a fadar shugaban kasa

- PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fito fili don yin bayani ga 'yan Najeriya ko za su samu kwanciyar hankali

Jam'iyyar PDP ta bukaci gamsasshen bayani game da harbin bindiga da aka ji a farfajiyar fada shugaban kasa da ka Aso Rock.

A wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, PDP ta yi ikirarin cewa ta samu rahotanni da ke bayyana an samu karantsaye ga tsaro a fadar shugaban kasa.

Hakan kuwa ta faru ne sakamakon hargitsi da rikicin da ya barke tsakanin iyalansa da ma'aikatan shugaban kasar.

A takardar da Jam'iyyar ta fitar tare da sa hannun kakakinta, Kola Ologbondiyan, ta ce ta matukar damuwa da abinda ya hada uwargidan shugaban kasar da hadimin mijinta har ya kai ga harbin bindiga.

Karar harbi a fadar shugaban kasa: PDP ta yi martani
Karar harbi a fadar shugaban kasa: PDP ta yi martani. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rikici tsakanin dan uwan Buhari da Aisha Buhari: An ji harbin bindiga a Aso Rock

"Jam'iyyar PDP ta damu matuka da rikicin da ya shiga tsakanin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari da hadiminsa wanda ya kai da fada har da harbin bindiga a fadar shugaban kasar," PDP ta kara da cewa.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa Aisha Buhari ta yi kiran gaggawa ga sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, da ya sako mata hadimanta da ke tsare a wurinsa.

Uwargidan shugaban kasar ta bada wannan umarnin ne a ranar Juma'a, 12 ga watan Yuni.

Aisha ta ce sakin hadimanta na da matukar amfani don karesu daga kamuwa da muguwar annobar korona yayin da suke tsare.

Ba ta bayyana takamaiman abinda ke faruwa a fadar shugaban kasar ba a wallafar da tayi a shafinta na Twitter.

Kamar yadda uwargidan shugaban kasa ta wallafa, "Cutar korona ba karya bace kuma tana nan a kasar nan babu shakka.

"Ina kira ga dukkan cibiyoyin gwamnati da al'amarin ya shafa, da su tabbatar da an bi dokar killace kai bayan an yi tafiya daga wata jiha zuwa wata.

"Duk wanda ya yi tafiya ya zama dole a tirsasa shi ya killace kansa na kwanaki 14 ko waye kuwa. Babu wanda ya fi karfin doka kuma 'yan sanda ne yafi cancanta su tuna hakan.

"Daga karshe, ina kira ga sifeta janar din 'yan sandan Najeriya da ya gaggauta sakin hadimai na da ke hannunsa don gujewa kamuwarsu da cutar korona a wurinsu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel