Atiku ya yi wa Obaseki tayin shiga PDP

Atiku ya yi wa Obaseki tayin shiga PDP

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi kira ga Godwin Obaseki, gwamnan jihar Oyo da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP, jaridar The Cable ta ruwaito.

The Cable ta gano cewa, Atiku ya tuntubi Obaseki a ranar Juma'a bayan hana shi takara da APC tayi a zaben gwamnan jihar Edo da ke zuwa a ranar 19 ga watan Satumba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, wanda shine dan takarar shugaban kasa a 2019 karkashin jam'iyyar PDP na nema wa Obaseki hanya mai sauki wurin sauya shekar zuwa jam'iyyar PDP.

Duk da kundun tsarin mulki ya bukaci mamban jam'iyya ya kwashe watannin 18 a kalla da yin rijista kafin ya fito neman kujerar siyasa.

Wata majiya mai kusanci da Atiku ta sanar da The Cable cewa tsohon dan takarar kujerar shugaban kasar ya tattauna da Obaseki a kan yuwuwar sauya shekar.

"Waziri na janyo hankalin Obaseki a madadin PDP. Ya yi magana da shi a jiya tare da bashi kwarin guiwa a kan ya komo PDP.

"Ya yi magana da wasu gwamnonin PDP tare da neman masa yadda zai samu masauki cikin sauki a jam'iyyar," majiyar tace.

Atiku ya yi wa Obaseki tayin shiga PDP
Atiku ya yi wa Obaseki tayin shiga PDP
Asali: UGC

KU KARANTA: Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake kashe wani basarake a Katsina

Crusoe Osagie, mai magana da yawun Obaseki bai yi martani a kan wannan maganar ba da aka tuntubesa a ranar Asabar.

The Cable ta ruwaito cewa akwai yuwuwar PDP ta zama matsayar gwamnan sakamakon hargitsi da rikici ya cika APC.

Rashin jituwa tsakanin gwamnan da Oshiomhole ya yi kamari tun bayan da ya hau mulkin jihar Edo.

Oshiomhole na goyon bayan Osagie Ize-Iyamu wanda a halin yanzu aka tantance lafiya kalau a jam'iyyar APC.

A jiya ne, jami'yyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da hana gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki daga shiga zaben fidda gwani na takarar zaben gwamna da za a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.

Shugaban, kwamitin tantance yan takarar, Jonathan Ayuba ne ya bayar da sanarwar a sakatariyar jamiyyar da ke birnin tarayya Abuja yayin da ya ke mika rahoto ga kwamitin gudanarwa (NWC).

Ayuba ya ce an kori Obaseki daga takarar ne saboda ya gabatar da sakamakon kammala karatun sakandare mai matsala.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel