Edo 2020: Dalilai 6 da suka sa APC ta haramta wa Obaseki takara
Kwamitin tantance 'yan takarar gwamnan APC na jihar Edo ta dogara da hana Obaseki takara da ta yi da dalilai shida, jaridar The Nation ta gano a daren Juma'a.
Wannan hukuncin ya matukar girgiza gwamna Obaseki wanda ya hanzarta sanar da cewa ba zai daukaka kara ba bayan hana shi tsayawa takara da aka yi.
Dalilan da suka sa aka hana Obaseki tsayawa takara kamar yadda The Nation ta gani daga kwamitin tantancewar a daren Juma'a sune:
1. Ikirarin mallakar satifiket din kammala makarantar gaba da sakandare (High school) wanda babu shi a tsarin karatun Najeriya.
2. Zarginsa da mallakar shaidar kotu wacce babbar kotun tarayya da ke Abuja ta musanta.
3. Kuskure a takardar shaidar kammala bautar kasa wacce ke dauke da Obasek a maimakon Obaseki.
4. Bacewar shaidar kammala firamare, sakandare da makarantar gaba da sakandare.
5. Karantsaye ga dokar kundun tsarin mulkin jam'iyya wacce ta haramta wa dan jam'iyya kai karar jam'iyyar kotu.
6. Dogaro da hukuncin kotun koli da kotun daukaka kara a kan banbance-banbance a suna.
Akwai hasashen da aka yi a daren jiya na cewa Obaseki zai sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP wacce ta ce kofarta bude take idan ya bukaci komawa.
Bangaren magoya bayan Obaseki na APC sun shirya yin taro a yau Asabar a garin Benin don yanke hukuncin mataki na gaba da za su dauka.
KU KARANTA: Adana kudi Abacha ya yi a kasashen ketare don kada mu jigata - Al-Mustapha
Obaseki wanda ya nuna ya rungumi kaddararsa, ya musanta cewa hukuncin kwamitin tantancewar na cike da rashin adalci, lamarin da yasa ya tabbatar da cewa ba zai daukaka kara ba.
Tun a shekaru biyu da suka gabata ne ake ta rikici tsakanin Oshiomhole da Obaseki.
Sauran 'yan takarar biyu da suka hada da: Chris Ogiemwonyi, tsohon karamin ministan ayyuka da Mathew Iduoriyekenwen, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Edo duk an hana su fitowa takara.
Har a halin yanzu ba a tabbatar da cewa Fasto Osagie Ize-Iyamu, Dr. Pius Odubu da Osaro Obazee za su yi takara a zaben fidda gwanin da za a yi a ranar 22 ga watan Yuni.
Tun a daren jiya kwamitin daukaka kara na jam'iyyar APC din ke jiran daukaka karar Obaseki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng