Rikici tsakanin dan uwan Buhari da Aisha Buhari: An ji harbin bindiga a Aso Rock

Rikici tsakanin dan uwan Buhari da Aisha Buhari: An ji harbin bindiga a Aso Rock

Kamar yadda majiya daga jami'an tsaro ta bayyana, an samu karantsaye a fannin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja a daren Alhamis.

Aisha Buhari tare da ADC dinta, Usman Shugaba sun yi kokarin saka karfi wajen tilasta mataimakin shugaba kasa na musamman, Sabiu Yusuf don killace kansa.

Majiya daga gidan gwamnatin tarayyar ta sanar da ThisDay cewa rikici ya fara ne bayan Sabiu, dan uwan shugaba Buhari ya dawo daga Legas.

Gidansa na kusa da fadar shugaban kasa amma sai bai killace kansa ba bayan dawowa daga tafiyar da yayi.

Dogaro da dokokin dakile annobar korona, majiyar ta ce uwargidan shugaban kasa, Zahra, Halima da Yusuf Buhari sun samu rakiyar wasu jami'an tsaro har da ADC dinta zuwa gidan Sabiu a daren Alhamis.

Bayan isarsu ne suka bukaci Sabiu wanda ake kira da Tunde, da ya killace kansa na kwanaki 14 don kada ya kawo musu annobar cikin iyalan.

Wannan lamari kuwa ya jawo sa'in'sa tsakaninsu inda Sabiu ya ce ba shine hadimi na farko da ya fara zuwa Legas ya dawo ba.

Hatta sabon shugaban ma'aikatan fadar, Farfesa Ibrahim Gambari na zuwa Legas duk kwanakin karshen mako kafin ya samu matsuguni a Abuja.

A don haka yake mamakin yadda suka tsananta masa da sai ya killace kansa bayan ziyarar matarsa da yayi bayan ta haihu.

KU KARANTA: An kwato yankunan da 'yan ta'adda suka kwace, jama'a sun koma gidajensu - Buhari

Sabiu, wanda aka fi sani da Tunde (ya samo sunan ne daga marigayi Janar Tunde Idiagbon, mataimakin Buhari yayin mulkin soji) ya koma gida bayan rikicin.

Shigarsa ke da wuya, uwargidan shugaban kasar ta shiga gidan tare da 'ya'yanta inda suka dinga cin zarafinsa.

Majiya daga fadar shugaban kasa wacce ganau ce ba jiyau ba, ta ce Sabiu ya tsallake katanga don barin gidan sakamakon harbin bindigar da ADC din Aisha Buhari ya yi a farfajiyar.

Daga bisani, Tunde ya samu shiga gidan Malam Mamman Daura inda ya kwana zuwa wayewar gari.

Jaridar ThisDay ta gano cewa, sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bada umarnin damke hadiman Aisha Buhari bayan rahoto da ya samu na tashin harbin bindiga a fadar shugaban kasar.

Daga ciki kuwa har da ADC Usman Shugaba. An damke su ne dogaro da cewa komai tsananin abinda ke faruwa bai dace su yi harbi a fadar ba don babban karantsaye ne ga tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: