Yadda mazauna Zaria suka yi murnar dawowar Sallar Juma'a

Yadda mazauna Zaria suka yi murnar dawowar Sallar Juma'a

- Jama'a mazauna karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna sun yi matukar farin cikin bude masallatan Juma'a a fadin jihar

- An gano cewa, da safiyar ranar Juma'a wurin karfe 8 ne yara da manya suka fara saka kayansu na alfarma don shirin sallar Juma'a

- Wani bawan Allah a garin ya bayyana cewa, da yawa daga cikin kananan yaransu sunkalla ranar Juma'a tamkar ranar Idi

Mazauna garin Zaria a ranar Juma'a sunyi murnar bude masallatan Jumaa a birnin Zazzau da wasu garurruwa da ke jihar ta Kaduna.

Tun misalin karfe 8 na safe ne mutane da dama suka yi wanka suka saka kayatattun kayansu domin shirin zuwa salla a masallatan Juma'a da suke raayin zuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kazalika wasu daga cikin masallatan suna kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka bayar da shawawarin a rika kiyaye wa domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Wani mazaunin Zaria, Malam Ibrahim Danllami ya ce mafi yawancin yara a birnin ta Zazzau sun dauki Juma'ar ta jiya tamkar ranar Sallar Idi ne a wurinsu.

Yadda mazauna Zaria suka yi murnar dawowar Sallar Juma'a
Yadda mazauna Zaria suka yi murnar dawowar Sallar Juma'a. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zaben Edo: Obaseki ya yi martani kan korarsa daga takarar gwamna a APC

A wani labari na daban, an sako Limamin da jami'an tsaro suka kama a kan jan sallar Juma'a a garin Zaria bayan kwanaki hudu da ya kwashe a wurin 'yan sanda.

A yayin da aka tuntubi limamin a yau Juma'a, Malam Muhammad Tukur ya ki yin tsokaci don ya ce Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa iqamatis Sunnah ta Zaria ta umarcesa da yayi shiru.

Amma kuma, ya tabbatar da cewa an sako shi a ranar Laraba bayan an kai shi gaban kotu. Bayan kama Idris da aka yi a ranar Juma'a, 22 ga watan Mayu, Malam Sani Yakubu, shugaban kungiyar JIBWIS reshen Zaria ya tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin.

Daya daga cikin mamun ya tabbatar da cewa sun yi sallar Juma'a din ne saboda watan Ramadana mai alfarma ne.

Ya kara da cewa: "Saboda bamu yi sallar Juma'a ba na makonni tara, mun bukaci Malam Tukur da ya ja mu sallar Juma'a a kalla ko ta karshe ce a watan Ramadana. Gaskiya ba shi ya shirya sallar ba.

"An rokesa ne kuma ya amince. Mu mutane ne masu son zaman lafiya don haka ne yasa muke biye wa dokokin gwamnati. Amma ba za mu zuba ido ana wulakanta malamanmu ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel