Brunei ta ce 'yan ƙasarta baza su samu ikon zuwa Saudiyya sauke farali a bana ba

Brunei ta ce 'yan ƙasarta baza su samu ikon zuwa Saudiyya sauke farali a bana ba

Kasar Brunei a ranar Laraba ta sanar da cewa yan kasarta ba za su samu ikon zuwa kasar Saudiyya ba domin yin aikin hajji ba a bana don fargabar annobar COVID-19 a cewar wata kafar watsa labarai na kasar.

Yayin taron manema labarai, Ministan harkokin addini na kasar, Awang Baddarudin Othman ya ce kasar ba za ta aike da maniyattan ta 1,000 da ta saba daukan dawainiyarsu duk shekara ba kamar yadda Borneo Bulletin ya ruwaito.

Musulmi a Brunei sun hakura da aikin hajjin bana
Musulmi a Brunei sun hakura da aikin hajjin bana. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Baddarudin ya ce an cimma wannan matsayar ne bayan Sultan Hassanal Bolkiah ya amince da shawarwarin da Cibiyar addinin musulunci ta Brunei ta bayar bayan taron da ta yi ranar Asabar da ta gabata inda ta soke daukan nauyin maniyattan bana.

DUBA WANNAN: Masari ya haramta bara a Katsina, ya yi wa islamiyoyi gargadi

Brunei ta zama kasa ta hudu a yankin Kudu maso Gabashin Asia da ta ce ba za tayi aikin hajji ba wannan shekarar bayan Singapore, Indonesia da Malaysia.

A watan Mayu, Singapore ta sanar da cewa yan kasar ta ba za suyi aikin hajjin bana ba saboda annobar coronavirus kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar Cibiyar harkokin addinin musulunci ta Singapore, maniyatta 900 da suka biya kudin kujerar zuwa aikin hajjin za su hakura sai shekarar 2021.

Ministan Harkokin Addini na Indonesia, Fachrul Razi, shima ya soke zuwa aikin hajjin na bana saboda fargabar annobar ta korona.

Kasar Indonesia ce ke da adadin maniyyata mafi yawa a duniya inda a bana mutum 221,00 suka ni niyyar zuwa kasar mai tsarkin domin sauke farali.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Gwamnatin Katsina ta hana barace-barace a fadin jihar kana ta yi wa makarantun allo da na islamiyya da ke jihar kashedin cewa har yanzu ba a basu damar cigaba da karatu ba.

Gwamnatin ta ce sassauta dokar kulle a jihar bai bayar da damar bude makarantu domin cigaba da karatu a cikinsu ba.

Sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Inuwa a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya ce an cimma zartar da wadannan matakan ne bayan bita kan halin da jihar ke ciki yayin wani taro.

Taron ya samu hallarcin wakilan gwamnati, hukumomin tsaro, malaman addinin musulunci, shugabannin addini da mambobin kwamitin kar ta kwana na yaki da coronavirus na jihar.

An gudanar da taron ne a Janar Muhammadu Buhari House kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce duk wanda aka kama yana bara zai fuskanci hukunci sannan malaminsa ko iyayensa suma za a hukunta su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel