PDP ce uwar jam'iyyu, har gobe ba zan barta ba - Jarumi Yakubu Muh'd
Daga cikin sanannun jarumai maza na Kannywood kuma mawaki a kasar nan, Yakubu Mohammed, ya ce har gobe yana nan daram a jam'iyyar PDP.
Yakubu Mohammed ya sanar da hakan ne yayin hirar da yayi da BBC a shafinsa na Instagram kai tsaye a ranar Laraba.
Jarumin ya taba batutuwa da dama da suka shafi manyan nasarorin da ya samu a fannin fina-finan da yayi da wakokinsa tare da alakarsa da abokansa na sana'a.
Jarumi Yakubu Mohammed ya tabbatar da cewa tun fara siyasarsa, jam'iyyar PDP yake goyon baya.
"Tunda farko, na fara da jam'iyyar PDP kuma har yanzu a ita nake," yace.
Dalilinsa na goyon bayan babbar jam'iyyar hamayyar shine, sun yi mata ayyuka masu yawa wanda hakan ne ya ja ra'ayinsa kuma ita ce uwar siyasa a Najeriya.
Ya kara da cewa, ya yi wa jam'iyyar wakokin siyasa amma wannan al'amarin bai yawaita a tare da shi ba saboda jakadancin hukumar zabe mai zaman kanta da yake yi.
Yakubu Mohammed ya ce a kaf Kannywood bashi da Uban gida. Shine Uban gidan kansa sai dai abokan arziki da yake da su.
Duk aminci da tsananin shakuwa da ke tsakanin jarumin mawakin da jarumi Sani Musa Danja, Yakubu Mohammed ya ce jarumi Ibrahim Mandawari ne ya fi burgesa a harkar fim.
KU KARANTA: Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo)
A wani labari na daban, fitaccen mawakin Hausa Nazifi Asnanic ya bayyana wa BBC cewa cikin tarihin wakokin da ya rera, ba zai taba mantawa da wakar da ya yi wa Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya ba.
Duk da dai mawakin ya ce ya fi kaunar wakar da ya yi wa Dr Rabiu Musa Kwankwaso, amma ya ce wacce ya yi wa Jonathan ta matukar tsaya masa a rai sakamakon halin da ya fada bayan nan.
Fitaccen mawakin ya sanar da hakan ne a hirar da yayi da BBC kai tsaye a shafinsu na Instagram. Kamar yadda yace, ya rera wa Jonathan waka ta yi karfi amma sai shekarar 2015 ta iso kuma "Masu son Buhari sun taru sun yi min yawa."
Asnanic ya ce a lokacin ya shiga rudani saboda wakar Jonathan ta ƙi bacewa, "ga shi kuma muna son mu yi tallan Buhari. Wannan ya sa ba zan iya mantawa da wakar ba," in ji shi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng