Rashin Tsaro: Zanga-Zanga ta sake barkewa a jihar Katsina

Rashin Tsaro: Zanga-Zanga ta sake barkewa a jihar Katsina

Daruruwan matafiya sun yi gamo da tasku a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, yayin da matasa suka datse titunan kauyen 'Yankara da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Fusatattun matasa sun sake sabunta zanga-zangar nuna bacin rai kan harin da 'yan ta'adda suka kai garuruwansu wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 60.

Sakamakon wannan zanga-zanga, matafiya da suka fito daga Kaduna, Zariya da Funtuwa, sun gaza samun damar wucewa ta titin da zai shigar da su Zamfara da Sakkwato.

Haka ma matafiyan da suka fito daga Kano suka ratso ta garin Sheme, sun makale a cunkuson da zanga-zangar ta haifar.

Fusatattun matasan sunyi burus sun yi wa jami'an tsaro kunnen uwar shegu bayan da suka nemi su bai wa matafiya hanyar wucewa.

Sun rike alluna mai dauke da sakon zargin gwamnatin tarayya da kuma hukumomin tsaro kan halin ko in kula da suka nuna dangane da matsalar rashin tsaro da ya addabe su.

Wani mazaunin garin 'Yankara, Abubakar Hamisu, ya ce su na gudanar da zanga-zangar ne domin nuna bacin ransu game da yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa.

Wata mata da ke kan hanyar Kano zuwa Gusau, Hajiya Zurfa Shugaba, ta ce ta yi murna da wannan zanga-zanga da matasan ke yi.

Zanga-Zangar da matasa su ka yi a kan hanyar Kankara zuwa Katsina
Hakkin mallakar Hoto: Daily Trust
Zanga-Zangar da matasa su ka yi a kan hanyar Kankara zuwa Katsina Hakkin mallakar Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ta ce "Bai kamata a rika zubar da jinin mutane da asarar rayuka kamar yadda ake samu a cikin 'yan lokutan nan ba. Dole ne sai gwamnati ta dauki mataki."

Haka kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, kwanaki kadan da suka gabata ne fusatattun matasa suka tare titin ‘Yantumaki, bayan 'yan ta'adda sun sace wani jami’in kiwon lafiya tare da ‘yar sa a garin.

KARANTA KUMA: Sarkin Katsina ya naɗa mai yiwa ƙasa hidima sabon hakimin 'Yantumaki

A ranar Talata matasan kauyen 'Yantumaki da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina sun gudanar da zanga-zanga makanmanciyar wannan.

Matasan dai sun datse titi sun yi zanga-zangar surfa wa Gwamnatin Jihar Katsina da ta Tarayya zagi, saboda matsalar tsaron da ta dabaibaye garin na ‘Yantumaki.

Sun yi kone-kone a babbar hanyar Kankara zuwa Katsina, lamarin da ya sanya dole matafiya su ka nemi wata hanyar da za su bi.

A jiya ne dai gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya yi wata doguwar ganawa da shugabannin tsaro na jihar a fadar gwamnatinsa da ke birnin Dikko.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel