Ba zamu kara saka dokar kulle ba - Gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da yasa ba lallai ta kara saka dokar kulle a kasa saboda hauhawar masu kamuwa da annobar korona ba.
Shugaban kwamitin kar ta kwana a kan annobar korona (PTF), sannan sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin taron hadin gwuiwa da kwamitin PTF ya saba gudanarwa.
"Kamar yadda na fada a baya, zamu sake duba na tsanaki a kan yanayin da ake ciki. Duk matakin da zamu dauka a nan gaba zai kasance bisa shawarar masana da kwararru a bangaren kimiyya da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
"Sannan dole mu duba halin da gwamnatinmu ke ciki, mu duba irin nasarorin da muke son cimma da kuma sake duban abubuwan da suka faru a tsawon sati biyar da aka yi a cikin dokar kulle," a cewar Boss Mustapha.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Malaman addini a karkashin inuwar United Muslim Foundation (UMS), a ranar Alhamis sun yi taro a Zaria don sake duba sharuddan dage dokar kulle a jihar Kaduna.
A yayin zantawa da manema labarai bayan taron da aka yi a cibiyar matasa da ke Tudun Wada, Zaria, Malam Tukur Isa, shugaban JIBWIS na jihar, ya ce sun amince da sharuddan.
Ya kara da cewa: "Amma kuma muna son yin amfani da wannan damar wurin sanar da gwamna cewa malaman addini ne ke da hakkin sanar da matsayarsu a fannin addini yayin annoba.
"A don haka, rashin mutuntawa ne a dinga bai wa malaman addini umarni wadanda suke wakiltar.
"A wannan lokacin na kulle, gwamnan yana kiranmu ne kawai ya bamu umarni kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana. Ba a taba tuntubarmu ba sai dai a bamu umarni.
"A matsayinmu na malamai, ya kamata gwamnan ya nemi sanin hukunce-hukunce a kan wasu al'amura.
DUBA WANNAN: 'Masana'anta ce' - Ahmed Lawan ya fadi sirruka a kan kungiyar Boko Haram
"Muna sanar da wannan ne don gwamnan ya dinga mutunta matsayarmu wacce ita ce wakilcin addini."
A dayan bangare, shugaban kungiyar, Malam Rabi'u Abdullahi, ya yi kira ga gwamnan da ya bude kasuwanni da makarantu don rufe su na ci gaba da matsantawa jama'ar jihar.
Abdullahi ya yi kira ga mazauna jihar da su tuba daga zunubansu.
Ya ce annobar Coronavirus ta samo asali ne daga zunubban mutane.
A ranar Talata ne gwamna El-Rufai ya dage dokar kulle a jihar Kaduna wacce ta kwashe kwanaki 75 tana aiki a don dakile yaduwar annobar Coronavirus.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng