Majalisar wakilai ta karrama jarumin dan sanda, DCP Abba Kyari (Hotuna)
Majalisar wakilan tarayya ta karrama hazikin dan sandan nan, DCP Abba Kyari, bisa namijin kokarin da yake yi wajen dakile yan bindiga da masu garkuwa da mutane a fadin Najeriya.
DCP Abba Kyari wanda ke jagorantar rundunar sifeto janar na yan sanda na leken asiri wato IGP-IRT ya taimaka matuka wajen ganin bayan dimbin masu garkuwa da mutane da suka addabi Najeriya.
Kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajbiamila ya bayyanawa yan majisar cewa za'a baiwa DCP Abba Kyari lambar yabo na musamman bisa jajircewarsa.
Daga cikin manyan masu garkuwa da mutanen da ya samu nasarar damkewa shina babban kasurgumi Chkwuemka Evans, anda biloniyan mai garkuwa ne wanda ya dade yana yi.
An dade ana neman Evans amma a ranar da dubunsa ta cika, rundunar Abba Kyari ta damkeshi a jihar Legas.
KU KARANTA: Ana baiwa hammata iska a majalisar dokokin jihar Kaduna (Bidiyo)

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng