'Masana'anta ce' - Ahmed Lawan ya fadi sirruka a kan kungiyar Boko Haram

'Masana'anta ce' - Ahmed Lawan ya fadi sirruka a kan kungiyar Boko Haram

- Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana damuwarsa a kan sabunta yawan kai hare - hare da kungiyar Boko Haram ta yi

- Sanata Lawan ya bayyana kungiyar ta'addanci ta 'yan Boko Haram a matsayin masana'anta

- A cewar Sanata Lawan, har yanzu mayakan kungiyar Boko Haram na cigaba da kaddamar da hare - hare a kan fararen hula

Sanata Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattijai, ya bayyana cewa kungiyar Boko Haram tana aiki tamkar wata masana'anta a Najeriya.

Da yake magana ranar Laraba, Sanata Lawan ya bayyana cewa yanzu kungiyar ta hada mambobi daga kasashe da addinai daban - daban, kamar yadda kafar watsa labarai ta AIT ta rawaito.

A cewar shugaban majalisar, duk kokarin majalisar dattijai na ganin an kawo karshen 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci, mayakan kungiyar Boko Haram sun cigaba da kasuwancinsu na ta'addanci domin cusa tsoro a zukatan 'yan Najeriya.

Sanata Lawan ya bayyana cewa har yanzu mayakan kungiyar Boko Haram na cigaba da kai hare - hare a kan fararen hula a yankin arewacin Najeriya.

"Yanzu Boko Haram ta tashi daga asalinta na kungiyar addini zuwa masana'anta. Ta koma masana'anta saboda yanzu babu alaka tsakanin abinda suke yi da kowanne irin addini.

'Masana'anta ce' - Ahmed Lawan ya fadi sirruka a kan kungiyar Boko Haram
Sanata Ahmed Lawan
Asali: Facebook

"Mutane ne da suka fito daga mabanbantan addinai, sannan daga kasashe daban - daban, sune suka tattaru yanzu da sunan kungiyar Boko Haram.

DUBA WANNAN: Hanyar Abuja: 'Yan bindiga sun kashe direbobi biyu, sun yi awon gaba da fasinjoji 16

"Majalisar dattijai ta sha kafa kwamiti a kan harkar rashin tsaro. Kwamitin wucin gadi na Sanata Kabiru Gaya ya jagoranta ya kewaya jihohin arewa da dama.

"Ni da kaina na taba jagorantar kwamiti da ya ziyarci jama'a a mazabu domin jin ta bakinsu a kan halin rashin tsaro, mun zauna tare da shugabannin hukumomin tsaro amma duk da haka rashin tsaro ya cigaba da zama babban kalubale a kasa," a cewar Lawan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel