Yanzu Yanzu: An tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna

Yanzu Yanzu: An tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna

Mambobin majalisar dokokin jihar Kaduna su 24 sun tsige mataimakin kakakin majalisar, Hon. Mukhtar Isa Hazo.

Lamarin ya biyo bayan wani zabe da aka yi na rashin amincewa dashi.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, ba a san takamaiman zargin da ake yi wa tsigaggen mataimakin kakakin majalisar ba.

A yanzu haka an nada Hon. Isaac Auta a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar dokokin, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: An tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna
Yanzu Yanzu: An tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna Hoto: The Nation
Asali: UGC

Auta ya kasance dan majalisa mai wakiltan Kauru.

An zabi Auta tare da rantsar dashi bayan wata yar hatsaniya ta kaure a zauren majalisar yayinda wani mamba ya yi kokarin sace sandar iko na majalisar.

A take sai magatakardar majalisar ya rantsar da Auta, wanda ya karbi rantsuwar kama aiki.

Jim kadan bayan rantsarwar, sai mamba mai wakiltan mazabar Makera, Hon. Liman Dahiru ya faso zauren majalisar sannan ya kwace sandar ikon.

Amma kafin ya yi nasarar ficewa daga zauren, sai sajen da ke wajen ya damke shi yayinda sauran mambobin majalisar suka yi saurin kwace sandar ikon daga hannunsa.

KU KARANTA KUMA: Korona: Gwamnan Abia ya bayyana halin da yake ciki a cibiyar killacewa

Daga nan sai hayaniya ya kaure a majalisar yayinda aka yi waje da fusataccen mamban, Dahiru Liman.

Daga baya an hango Liman, wanda rigarsa ta yayyage a wajen zauren inda yake nuna fushinsa a kan tsige Hazo.

A wani labarin na daban, mun ji cewa an dakatar da daraktan cibiyar lafiya ta jihar Nasarawa, Samuel Atala saboda satifiket na bogi.

Shugaban hukumar kula da asibitocin (NAPHDA), Dr Mohammed Usman Adis, ya ce cibiyar ta yi biyayya ne ga majalisar jihar yadda ta dakatar da Atala a matsayin darakta har sai an kammala bincike a kan shaidun kammala makarantarsa.

Ya sanar da hakan ne bayan gurfana da yayi a gaban kwamitin majalisar jihar Nasarawa a ranar Talata a garin Lafia.

Ya ce cibiyar ta mika takarda ga jami'ar jihar Binuwai a kan satifiket din kuma tana jiran martanin jami'ar.

Shugaban cibiyar ya ce za su ci gaba da adalci ga dukkan ma'aikatansu a bangaren karin girma don tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: