Boko Haram: Buhari zai gana da shugabanin majalisa da shugabanin tsaro

Boko Haram: Buhari zai gana da shugabanin majalisa da shugabanin tsaro

Majalisar Dattijai a ranar Alhamis ta wajabtawa shugabanin ta ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabanin hukumomin tsaron kasar game da sabbin hare haren da Boko Harm ke kai wa.

An cimma wannan matsayar ne bayan Sanata Abubakar Kyari mai wakiltan Borno ta Arewa ya yi magana game da kashe mutum 90 da yan taaddan suka yi a baya bayan nan a mazabarsa.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatain tarayya ta umurci Sojojin Najeriya su tabbatar da tsaro a yankin Tafkin Chadi cikin gaggawa.

Boko Haram: Buhari zai gana da shugabanin majalisa da shugabanin tsaro
Boko Haram: Buhari zai gana da shugabanin majalisa da shugabanin tsaro. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa hadimin Aisha Buhari rasuwa

Har wa yau, Majalisar ta bukaci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA) da Hukumar Cigaban Yankin Arewa ta Gabas (NEDC) su gaggauta kaiwa mutanen da harin ya shafa dauki.

Kazalika, ta umurci gwamnatin tarayya ta aiwatar da shawarwarin da Majalisar Dattijai ta bayar da inganta tsarin tsaro a Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan ya yi alkawarin tuntubar takwarorinsu na Majalisar Wakilai na Tarayya domin su tafi su gana da Buhari da shugabanin hukumomin tsaron.

Ya jaddada cewa duk wani shugaban hukumar tsaro da ya gaza wurin gudanar da aikinsa duk da an samar masa da kayan aiki zai rasa aikinsa.

Ku dakaci cikaken rahoton ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel