Filato: Masu hakar kabari sun koka a kan yawan mace-mace

Filato: Masu hakar kabari sun koka a kan yawan mace-mace

A ranar Laraba ne masu hakar kabari a garin Jos suka bayyana cewa sun birne sama da gawawwaki 100 a makabartar da ke kan titin Zaria da kuma Narkuta a makonni shida da suka gabata zuwa yanzu.

Bashir Muhammad da Haruna Bala shugabannin makabartun ne da suka yi bayanin abinda ke faruwa ga jaridar Daily Trust.

Sun ce daga ranar 23 ga watan Afirilu zuwa 3 ga watan Mayu, sun birne gawawwaki 56. Sun kara birne wasu gawawwaki 49 daga ranar 4 ga watan Yuni zuwa 10 ga wata.

Jimillar sun kai 105 a cikin makonni shida kacal, jaridar daily Trust ta ruwaito.

Daga cikin gawawwaki 49, 37 an birnesu ne a makabartar kan titin Zaria yayin da aka birne sauran 12 a makabartar Narkuta.

A yayin kirga sabbin kaburburan, Muhammad ya tabbatar da cewa da yawa daga cikin mamatan manyan magidanta ne wadanda cutar yunwa ta kashe.

"Da yawa daga cikin 'yan uwan mamatan sun sanar da su cewa Ulsa ce ta kashesu.

"Amma kuma akwai barkewar wata annoba da ke kashe mutane kamar yadda jama'ar garin ke fadi," yace.

Filato: Masu hakar kabari sun koka a kan yawan mace-mace
Filato: Masu hakar kabari sun koka a kan yawan mace-mace. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta

Shugaban karamar hukumar Jos ta arewa, Shehu Bala, a yayin da ya zanta da Unity FM a ranar Laraba, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma bai danganta shi da wata sabuwar cuta ba.

Ya kara da cewa ya mika littafi ga masu hakar kabarin don su dinga rubuta sunayen mamatan idan an kawo su don birnewa.

Kwamishinan lafiya na jihar Filato, Nimkong Larndam, wanda ya tabbatar da aukuwar mutuwar, ya ce babu wani tabbaci a kan abinda ya kawo mace-macen amma gwamnati na kokarin bincike a kan lamarin.

Wata babbar likita mai suna Dr Fatima Gyaran a Jos, ta ce tana da masaniya a kan sabbin mace-macen da suke faruwa a garin.

"Na samu labarin cewa ciwon sukari ya kashe mutum biyu. Babu dangantaka tsakanin mace-macen da wata sabuwar cuta," tace.

Wannan na zuwa ne bayan barkewar annobar korona a fadin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng