Yanzu-yanzu: Gwamna Zulum ya bada umurnin bude makarantu a Bama

Yanzu-yanzu: Gwamna Zulum ya bada umurnin bude makarantu a Bama

Gwamnan jihar Borno, Farsesa Babagana Umara Zulum, ya bada umurni bude makarantun sakandare uku kuma dalibai su koma makaranta a karamar hukumar Bama.

Jawabi daga gidan gwamnatin jihar ya bayyana cewa Zulum yayi wannan sanarwa ne yayinda ya kai ziyara Bama, Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya tafi raba kayan abinci da sauran kayan alfanu ga al’ummun dake cikin halin bukata a garin.

Bayan kammala rabon kayan masarufin, gwamnan ya sanar da bude makarantun sakandare uku dake Bama saboda dalibai su cigaba da karatunsu.

Zulum Yace: “Nan da ba dadewa ba zan dawo. Da kaina zan duba daukan dalibai. Ya zama wajibi mu bude makarantun sakandarenmu.”

”Zamu mayar da da babbar makarantar nan ta koma ta sakandare, yayinda makarantar sakandaren mata za ta koma makaranta makarantar firamaren Shettmari na dan wani lokaci”

Jihar Borno ce jiha ta farko da zata bude makarantu bayan kullesu da akayi sakamakon cutar Coronavirus.

Legit Hausa ta rahoto muku cewa Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 663 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.45 na daren ranar Talata 9 ga Yuni na shekarar 2020.

A yanzu haka, jihar Borno na jinyar mutane 136 masu fama da cutar yayinda tara (9) sun rigamu gidan gaskiya.

Karin sabbin mutum 663 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka; Lagos (170), Ogun (108), Bauchi (69), Ebonyi (49), Edo (33), Rivers (30), FCT (26), Jigawa (26), Delta (20), Anambra (17), Gombe (16), Kano (16), Imo (15), Abia (14), Borno (11), Oyo (11), Plateau (8), Kebbi (6), Kaduna (6), Ondo (4), Niger (2), Katsina (2), Osun (1), Ekiti (1), Kwara (1), Nasarawa (1).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel