Cristiano Ronaldo zai bar Juventus a karshen kakar bana - Balzano
- Ana yayata jita-jitar cewa Cristiano Ronaldo zai yanke hulda da Kungiyar Juventus a karshen kakar wasanni ta bani
- Dan wasan mai shekaru 35 a duniya ya ya kasance tauraron kungiyar Juventus a kakar wasanni biyu da suka gabata
- Sai dai rahoton da wani dan jarida na kasar Italiya, Pietro Balzano Porta ya ruwaito, ya yi ikirarin cewa Ronaldo zai bar kungiyar Juventus a karshen kakar wasannin bana
A wani rahoto mai cike da ban mamaki da daukar hankali, an ruwaito cewa, Cristiano Ronaldo zai bar kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke kasar Italiya a karshen kakar wasanni ta bana.
Ana rade-radin cewa, dan wasan gaban wanda tauraruwarsa ke ci gaba da haskawa, ya yi shirin cika bujensa da iska daga kasar Italiya da zarar an karkare gasar wasannin bana.
Wani mashahurin dan jarida na kasar Italiya, Pietro Balzano Porta, shi ne ya yi ikirarin hakan a wani sako da wallafa kan shafinsa na Twitter.
Dan jaridar ya wallafa sakon ne cikin harshen Italiya tun a ranar 27 ga watan Mayun 2020.
Balzano ya ce fitaccen dan wasan na kasar Portugal zai kara gaba daga kungiyar Juventus a karshen kakar wasannin bana.
A baya- bayan nan an samu sa'insa tsakanin Ronaldo da Kocin Juventus, Maurizio Sarri, bayan ya sauya shi a wasansu na gasar Serie A da suka fafata da kungiyar AC Milan.
KARANTA KUMA: Kashi 43% na talakawan duniya suna zaune a Indiya, Najeriya da Jamhuriyar Congo - Bankin Duniya
Hakan ya sanya Ronaldo cikin fushi ya fice daga filin wasan na Allianz saboda kishin rashin zura kwallo a koma ganin cewa an sauya shi tun babu ci a wasan.
Ana iya tuna cewa, Paulo Dybala, wanda ya canji Ronaldo a wasan, shi ne ya zura kwallon da ta tabbatar da nasarar kungiyar Juventus a wasan tun a minti na 77.
Daga bisani Ronaldo ya ba da hakurin abinda ya faru a baya tsakaninsa da mai horas da 'yan wasan na kungiyar Juventus, kuma tauraruwarsa ta ci gaba da haskawa a kamar koda yaushe.
A halin yanzu Ronaldo ya jefa kwallaye 53 a kungiyar Juventus tun bayan barin kungiyar Real Madrid da ke kasar Spain a shekarar 2018.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng