Da duminsa: Makarantarmu Obaseki ya yi karatun digirinsa - Jami’ar Ibadan UI

Da duminsa: Makarantarmu Obaseki ya yi karatun digirinsa - Jami’ar Ibadan UI

Jami’ar farko a Najeriya, jami’ar Ibadan wacce aka fi sani da UI ta fito ta raba gardama kan cece-kucen da akeyi kan sihhancin kwalin karatun gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Jami’ar ta bayyana cewa lallai a cikinta gwamnan ya kammala karatun digirinsa na farko kuma an yaye shi.

Jami’ar ta bayyana hakan ne a jawabin da Rijistra, Mrs Olubunmi O Faluyi, ta saki ranar Laraba.

A jawabin, gwamnan ya samu admishon shiga jami'ar a shekarar 1976 kuma ya kammala a shekarar 1979 da darajar 'Jamil Jiddan Munkhafid (2nd Class Lower).

"Takardun shaidar shiga da yayesa na nan ajiye a asusun ajiyar jami'ar." Cewar jawabin.

Wasu yan adawar gwamnan a jihar suna tuhumar gwamnan da gabatar da kwalin digirin bogi. Sun yi zargin cewa bai kammala karatu a jami'ar ba.

Da alamun wannan jawabi da jami'ar ta saki zai kawo karshen zarge-zargen.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya sake shan kaye a kotu, an tabbatar da Sanatan APC

Da duminsa: Makarantarmu Obaseki ya yi karatun digirinsa - Jami’ar Ibadan UI
Jami’ar Ibadan UI
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana ranar Laraba cewa shugaban jamiyyar All Progressives Congress APC , Mr Adams Oshiomhole, da gwamna Godwin Obaseki, sun yi cacar baki kan sihhancin digirin gwamnan daga jami’ar Ibadan.

Oshiomole yayin rantsar da kwamitin tantance yan takaran zaben fiddan gwanin jamiyyar ya bayyana cewa akwai shakku cikin sihhanci digirin da gwamnan ke ikirarin ya karanta.

Amma gwamnan ta bakin mai magana da yawunsa, Crusoe Osagie, ya kalubalanci Oshiomole ya je jami’ar Ibadan ya tambayesu sihhancin digirinsa.

Shi kuma ya kalubalanci Adams Oshiomole ya bayyanawa yan Najeriya jami’ar da ya halarta.

Rikicin dake tsakanin Adams Oshiomole da magajinsa gwamna Obaseki yaci tura duk da yunkurin gwamnonin APC da Alhaji Aliko Dangote wajen sulhuntasu.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta wallafa salon zaben fidda gwanin yan takara na zaben gwamnan jihar Edo.

Yayinda dukkan sauran jam'iyyu 15 da zasu yi zaben suka zabi salon yar tinke, jam'iyyar dake kan ragamar mulki, APC ta zabi salon 'kato bayan kato'

Da alamun za'a fuskanci sabon rikici saboda gwamna Obaseki ya lashi takobin ba zai amince a bi salon 'kato bayan kato' ba a jiharsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel