Matawalle ya bawa tsohon ɗan takarar gwamnan APGA muhimmin muƙami

Matawalle ya bawa tsohon ɗan takarar gwamnan APGA muhimmin muƙami

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya nada Dr Sani Shinkafi matsayin mai bada shawara na musamman a gwamnatinsa

- Dr Sani Shinkafi tsohon sakataren jam'iyyar APGA ne na kasa kuma ya yi takarar kujerar gwamnan jihar a 2019

- Gwamna Matawalle ya ce tsananin cancanta ya duba tare da gudumawar da ya ga Shinkafi ya bada wajen dawo da zaman lafiya a jihar

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya nada tsohon dan takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APGA, Dr Sani Shinkafi matsayin mai bada shawara tsakanin al'amuran gwamnatoci.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da sakataren gwamnatin jihar, Bala Bello ya sa hannu a Gusau a ranar Laraba.

Gwamnan ya ce ya yi wannan nadin ne sakamakon kwazo da bautawa kasa da Shinkafi yayi tare da gudumawar da ya bada wurin kawo zaman lafiya a jihar.

"A matsayin Shinkafi na mamba a kwamitin shawo kan matsalar 'yan bindiga, ya bai wa gwamnati goyon baya wurin samar da zaman lafiya a jihar," yace.

An haifa Dr Sani Shinkafi a karamar hukumar Shinkafi ta jihar sannan ya halarci makarantar firamare a garin tsakanin 1976 zuwa 1982.

Ya yi aiki da ma'aikatar noma da ma'adanai tare da aiki a matsayin akanta a tsohuwar jihar Sokoto.

Shinkafi ya kai matsayin odita a ma'aikatar kafin ya koma mataimakin mukaddashin darakta.

Kafin wannan nadin, yana matsayin darakta a Patriots for the Advancement of Peace and Social Development, kungiyar taimakon kai da kai.

Matawalle ya bawa tsohon ɗan takarar gwamnan APGA muhimmin muƙami
Matawalle ya bawa tsohon ɗan takarar gwamnan APGA muhimmin muƙami. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Shinkafi wanda tsohon sakataren jam'iyyar APGA ne na kasa, ya fito takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara a 2019.

A wani labari na daban, kwamishinoni uku sun kamu da cutar coronavirus (COVID-19) a jihar Gombe kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kwamishinan labarai da al'adu na jihar, Ibrahim Alhassan ne ya sanar da manema labarai a ranar Talata.

Ya ce an gano kwamishinonin sun harbu da kwayar cutar ne bayan an yi wa kwamishinoni 21 na jihar da hadiman gwamna gwaji.

Alhassan ya kuma tabbatar da cewa daya daga cikin hadiman gwamnan da 'yan majalisar jihar Gombe 5 sun kamu da kwayar cutar ta korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel