Karin mutum 663 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 13,464

Karin mutum 663 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 13,464

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 663 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.45 na daren ranar Talata 9 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 663 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-170

Ogun-108

Bauchi-69

Ebonyi-49

Edo-33

Rivers-30

FCT-26

Jigawa-26

Delta-20

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Anambra-17

Gombe-16

Kano-16

Imo-15

Abia-14

Borno-11

Oyo-11

Plateau-8

Kebbi-6

Kaduna-6

Ondo-4

Niger-2

Katsina-2

Osun-1

Ekiti-1

Kwara-1

Nasarawa-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Talata 9 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 13464.

An sallami mutum 4206 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 365.

A wani rahoton, kun ji cewa Kwamitin yaki da COVID-19 ta shugaban kasa, PTF ta ce akwai yiwuwar yanzu ne annobar korona ta fara yaduwa a Najeriya.

PTF ta koka kan yadda yan Najeriya suke gudun zuwa yin gwajin wadda hakan yasa har yanzu mutane kalilan aka yi wa gwajin idan aka kwatanta da adadin mutanen da ke kasar.

An sanar da hakan ne yayin da mambobin PTF suka bayyana a gaban kwamitin hadaka ta majalisar wakilai da dattijai domin yi musu bayani kan yadda aka kashe kudaden da aka bawa Najeriya tallafi don yaki da corona.

Shugaban PTF, kuma sakataren gwmanatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana fargabansa kan rashin sanin yadda annobar za ta kasance inda ya roki 'yan majalisar su taimaka wurin wayar da mutane a mazabansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel