Annobar korona: Sanata Ndume ya bukaci FG ta rage albashin ma'aikata
Ali Nudume, sanata mai wakiltar mazabar jihar Borno ta kudu, ya bukaci gwamnatin tarayya ta zabtare albashin ma'aikata.
Da ya ke magana a wani shirin gidan talabijin na 'Channels', Ndume ya ce bai kamata gwamnati ta ke biyan ma'aikata cikakken albashi ba, saboda yanzu a zaune kawai suke a gida.
Ndume, mamba a jam'iyyar APC, ya bukaci gwamnati ta bawa ma'aikata tallafi idan tana so su zama masu sadaukarwa, da zasu rungumi ragin albashin.
"Ya kamata gwamnati ta yi duba na tsanaki a kan kudaden da take kashewa a kan ma'aikata, wanda ke lashe kusan kaso 70% na kasafin kudi. Akwai bukatar a ingiza kudi domin kaddamar da manyan aiyukan raya kasa.
"Ya kamata mutane su kasance masu sadaukarwa. Wannan lokacine na sake duban al'amura da natsuwa.

Asali: Facebook
"Sai dai, duk lokacin da na yi magana irin wannan, jama'a su kan fito su sokeni tare da kirana sunaye marasa dadi. Amma hakan ba zai hana na fadi ra'ayina ba.
DUBA WANNAN: Rabon tallafin annobar korona: Matawalle ya caccaki minista Sadiya Farouk
"Akwai bukatar sadaukarwa, musamman a bangaren ma'aikata. Ma'aikata basa zuwa aiki amma ana biyansu cikakken albashi, ana cigaba da kashe musu kudi kamar a lokacin da suke aiki.
"Akwai wani uzuri na cigaba da kashe kudi a kansu? idan mutum ba zai iya aiki a cikin annoba ba, sai a bashi tallafi, a rage masa albashi," a cewar Sanata Ndume.
Gwamnatin tarayya ce ta umarci ma'aikata su zauna a gida domin dakile yaduwar annobar cutar korona.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng