Rabon tallafin annobar korona: Matawalle ya caccaki minista Sadiya Farouk

Rabon tallafin annobar korona: Matawalle ya caccaki minista Sadiya Farouk

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya caccaki ministar ma'aikatar harkokin hidimatawa 'yan kasa tare da bayyana kalamanta a kan rashin tsaro a matsayin zallar rashin adalci ga gwamnatinsa.

A ranar Asabar ne, Sadiya Umar Farouk, ministar ma'aikatar harkokin hidimtawa 'yan kasa ta isa jihar Zamfara domin rabon tallafin rage radadin matsin da annobar cutar korona ta haifar ga talakawa.

Sai dai, jim kadan bayan saukarta a Zamfara domin kaddamar da fara rabon tallafin, ministar ta fice daga jihar tare da dakatar da kaddamar da fara rabon tallafin, tana mai kafa hujja da cewa babu tsaro a jihar.

A martanin da ya yi saurin mayar mata, gwamnan jihar Zamfara ya bayyana kalaman ministar a matsayin marasa tushe tare da bayyana cewa akwai zaman lafiya a jihar.

A cikin jawabin da ya fitar ta bakin kakakinsa, Zailani Bappa, gwamnan ya ce: "tabbas jihar Zamfara na fuskantar kalubalen tsaro kamar sauran wasu jihohin arewa, amma namijin kokarin gwamna Matawalle ya kawo ingantar tsaro a cikin shekara guda da ta gabata.

"Ita kanta ministar ta san cewa yanzu an samu saukin matsalar rashin tsaro a jihar zamfara idan aka kwatanta da baya.

"Ba a rasa wasu 'yan matsaloli lokaci zuwa lokaci, kamar irin abinda ya faru a Talata Marafa a makon jiya, amma, bayan haka, yanzu jama'a sun fi sakewa da samun kwanciyar hankali yayin da suka fita domin gudanar da harkokinsu.

Rabon tallafin annobar korona: Matawalle ya caccaki minista Sadiya Farouk
Minista Sadiya Farouq yayin rabon tallafi a Abuja
Asali: Facebook

"Gwamnatin jihar Zamfara ba zata yi shakka ba wajen sanar da cewa rashin tsaro bai taba hana wani taron gwamnati ko na kungiyoyi ba tun bayan hawan gwamna Matawalle, shekara guda da ta gabata," kamar yadda ya ke a cikin jawabi.

Kazalika, gwamnan ya musanta cewa ya share ministar tare da kin karramata yayin da ta isa jihar Zamfara domin kaddamar da rabon kayan tallafin.

DUBA WANNAN: Afrika ta Kudu da sauran kasashen Afrika 7 da tattalin arzikin Najeriya ya doke nasu a bana

"Ranar Asabar ta iso jihar Zamfara kuma gwamna Matawalle ya karramata da masauki da duk abinda take bukata tare da tura sakataren gwamnatinsa ya yi mata maraba.

"Amma, sai ga shi a ranar Lahadi an sanar da gwamna cewa ministar ta koma Abuja ba tare da yin abinda ya kawota jihar ba.

"Rashin adalci ne a zargi gwamna Bello da share ministar ko rashin karramata, kamar yadda wasu rahotanni ke bayyanawa," a cewar Zailani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel