Dalilin da yasa ba za mu bude makarantu yanzu ba – FG

Dalilin da yasa ba za mu bude makarantu yanzu ba – FG

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba za ta bude makarantu ba a yanzu ba domin har yanzu akwai hatsari tattare da yin hakan.

Karamin ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja yayin jawabin kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19, PTF.

Ya karyata jita jitar da ake yadawa na cewa gwamnati za ta bude makarantu a ranar 21 ga watan Yunin shekarar 2020 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dalilin da yasa ba za mu bude makarantu yanzu ba – FG
Dalilin da yasa ba za mu bude makarantu yanzu ba – FG. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Ya ce, "Dole mu nemi shawarwarin kwararru kafin bude makarantu a kan lokacin da ya dace.

"Hakan ya zama dole don kwace wa kuskuren saka dalibai zuwa makaranta kuma su dawo gida."

Ya ce maaikatar ba za ta jefa yan Najeriya cikin hatsari ba kawai domin gaggawar son bude makarantu.

"Ba zan so inyi gwaji da yayan ku ba.

"Abinda muke son yi shine mu kawo wadanda za su rubuta jarrabawar fita daga karamar sakandare da wadanda za su rubuta jarrabawar kammala WAEC.

"Muna laakari da lokacin da jihohi za su bude iyakokinsu domin daliban su samu damar tafiya makarantu su rubuta jarrabawar," in ji shi.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban PTF, Boss Mustapha ya ce Najeriya ba za tayi gaggawar bude makarantu ba saboda kare afkuwar abinda ya faru a wasu kasashe.

Ya bayar da misali da kasar Korea ta Kudu da ta bude makarantu amma dole ta rufe bayan cutar da sake bulla.

Ya kara da cewa, "Ita ma kasar Israila a kwana kwanan nan ta bude makarantu amma dole ta rufe.

"Sobada haka, ya kamata mu dauki darasi daga abinda ya ke faruwa da wasu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel