Bayyana kadarori: SERAP ta maka Buhari da Osinbajo a Kotun daukaka kara

Bayyana kadarori: SERAP ta maka Buhari da Osinbajo a Kotun daukaka kara

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da rashawa a Najeriya, ta shigar da karar shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo a kotun daukaka kara.

Kungiyar SERAP ta na neman duk masu rike da madafan iko da manyan ma'aikatan gwamnati a kasar nan da su bayyanawa duniya adadin dukiya da kadarorin da suka mallaka.

SERAP ta na neman kotun ta tursasa wa Kotun da'ar ma'aikatan Najeriya CCB, bayyana wa duniya kadarorin da shugaban kasa, mataimakinsa da gwamnoni 36 da mataimakansu suka mallaka.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, a baya bayan nan SERAP ta yi kicibus da tangarda yayin da wata babbar kotun tarayya a jihar Legas ta yi watsi da wannan bukata da ta shigar.

Bayyana kadarori: SERAP ta maka Buhari da Osinbajo a Kotun daukaka kara
Bayyana kadarori: SERAP ta maka Buhari da Osinbajo a Kotun daukaka kara
Asali: UGC

Da ta ke bayyana rashin jin dadi game da hukuncin da Mai shari'a Muslim Hassan ya yanke, SERAP cikin wata sanarwa da fitar a ranar Lahadi, ta ce ta garzaya kotun daukaka kara.

KARANTA KUMA: An dakatar da dokar cin gashin kan majalisu da bangaren shari’ar jihohi bayan ganawar Buhari da gwamnoni

Sanarwar da ta fito daga bakin mataimakin darekta na kungiyar, Kolawole Oludare, ta ce Jastis Muslim ya yi wa dokar da Majalisar Tarayya ta kaddamar a shekarar 2011 kuskuren fahimta.

SERAP ta ce mai shari'a Muslim bai yi la'akari da dokar 'yancin bayanai ba, FOI, wadda ta yarjewa al'umma sanin duk wani bayani a kan masu rike da madafan iko.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Kimanin watanni biyar da suka gabata, Legit.ng ta ruwaito cewa, SERAP ta aikewa da shugaba Buhari da mataimakinsa wasikar neman su bayyanawa duniya dukiyoyinsu.

Kungiyar ta nemi bayani a kan kadarorin da suka mallaka; ta na mai cewa rashin bayyana wa al'umma dukiyarsu a fili ba ya taimakon gaskiya da kuma rikon amana.

A cewar SERAP, alkawarin da shugaba Buhari ya yi wa jama’a yayin yakin neman zabe na cewa zai bayyanawa duniya abin da ya mallaka, ya sa ta aiko masa wannan takarda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel