Harkallar filaye: Kotu ta yi watsi da karar tubabben Sarki Sanusi

Harkallar filaye: Kotu ta yi watsi da karar tubabben Sarki Sanusi

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Litinin ta kori karar da tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, wacce ke bukatar dakatar da bincikar zargin wata almundahanar filaye da masarautar jihar Kano ta yi.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, a ranar 6 ga watan Maris din 2020 ne tsohon basaraken ya tunkari kotun da bukatar cewa a dakatar da Ganduje, antoni janar da kuma shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar a kan bincikarsa.

Korafin ya bukaci kotun da ta dakatar da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano da shugabanta, Muhyi Rimingado, da ya dakata da bincikarsa har sai an kammala shari'ar farko.

Alkali mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ya yanke hukuncin cewa, hukumar ba ta take wani hakki na tsohon basaraken ba na bincikarsa a kan zargin da ake masa.

Daga nan Allagoa ya yi watsi da karar, tare da tabbatar da cewa babu wani hakkin na Sanusin da aka yi wa karantsaye.

A yayin sanar da sakamakon zaman kotun, Abubakar Ibrahim, babban mataimaki na musamman ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, "Babban kotun tarayyar karkashin mai shari'a Allagoa ya yi watsi da bukatar tsohon sarkin Kanon a kan PCACC.

"A hukuncin da ya yanke a yau Litinin, 8 ga watan Yuni, kotun ta bai wa hukumar yaki da rashawa da ta ci gaba da bincikar tubabben sarkin."

Harkallar filaye: Kotu ta yi watsi da karar tubabben Sarki Sanusi
Harkallar filaye: Kotu ta yi watsi da karar tubabben Sarki Sanusi. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, tubabben hakimin Gabasawa tun zamanin mulkin Marigayi Ado Bayero, Amin Babba Dan'agundi, ya ce zai ci gaba da addu'a ga Allah da ya bi masa hakkinsa sakamakon zaluntarsa da aka yi.

Tubabben basaraken, ya bayyana hakan ne bayan hukuncin da kotun kolin Najeirya ta yanke bayan shekaru 17 da tube masa rawani.

A tattaunawar da BBC ta yi da basaraken bayan hukuncin kotun kolin, tsohon basaraken ya ce ko da ya so karbar hakkinsa, amma hukuncin Allah ya fi masa.

Ya kara da cewa, bai taba tsammanin rashin nasara ba a karon karshe don kuwa duk kotunan da ya je a baya shi ya yi nasara.

"Na karba wannan hukuncin kuma bani da ja a kai. Amma duk wanda ya ke gani ya taka wata rawar gani, na bar shi da Allah.

"Tun farko hakkina na bukata kuma har yanzu ina nan zan gaya wa Allah ya yi min sakayya," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel