Takarar shugaban kasa a 2023: PDP ta mayarwa da dan Atiku martani
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa tsarin karba - karba ne kadai zai nuna makomar yiwuwar takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
An fara maganganu a kasa a kan cewa Atiku zai fito takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Adamu Atiku-Abubakar, ‘dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce mahaifinsa zai sake fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Jaridar Punch ta ce Alhaji Adamu Atiku-Abubakar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya ke bayani a game da nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a jihar Adamawa.
A makon da ya gabata ne Adamu Atiku-Abubakar ya shafe shekaru guda a ofis a matsayin kwamsishinan ayyuka a karkashin gwamnatin PDP ta Ahmadu Finitiri.
Da ya ke bayani a game da nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a shekara guda, Adamu Atiku-Abubakar, ya yi magana game da siyasar Najeriya da kuma zaben 2023.

Asali: Facebook
Ya ce: “Ni a karon kai na, ban ga wani laifin mahaifina ya fito takarar kujerar shugaban kasa ba. A 2023, mahaifina (Atiku Abubakar) zai yi harin kujera mai darajar farko a kasar nan.”
Da ya ke bada dalilansa, sai ya ce: “Saboda (Atiku) ya kasance kwararren ‘dan siyasa, mai dabara, uban gida, wanda ya kuma lakanci harkar siyasa na kusan shekaru 40.”
DUBA WANNAN: Abin da El-Rufa'i ya fada a kan salon mulkin shugaba Buhari
Atiku ya yi takarar neman kujerar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2019, amma sai ya sha kasa a hannun shugaba Muhammadu Buhari, dan takarar jam'iyyar APC.
Da ya ke magana yayin wani taro da manema labarai a Abuja, sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya ce; "PDP ba ta yanke wata shawara ba a kan tsarin karba - karba. Iya abinda zan iya fada kenan a halin yanzu."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng