An yi wa matashi 'dukan kawo wuka' a kan yi yarinya mai shekaru 7 fyade

An yi wa matashi 'dukan kawo wuka' a kan yi yarinya mai shekaru 7 fyade

- Matashi dan shekara 26 ya sha da kyar bayan ya yi lalata da karamar yarinya mai shekaru 7

- An kama mutumin mai suna Patrick Onoja Igah yana lalata da yarinya mai shekaru bakwai a farfajiyar coci

- An yi mishi dukan kawo wuka har an kusan kashe shi kafin 'yan banga su kwace shi tare da mika shi hannun 'yan sanda

Wani matashi mai shekaru 26 ya tsallaka rijiya da baya a cikin kwanakin karshen mako bayan da ya lalata yarinya mai shekaru bakwai.

Fusatattun mazauna kauyen Akparoji da ke yankin Owukpa na karamar hukumar Ogabdigbo na jihar Benue ne suka yi yunkurin banka masa wuta.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, an kama mutumin mai suna Patrick Onoja Igah yana lalata da yarinya mai shekaru bakwai a farfajiyar coci.

Mazauna yankin sun ce, Ogah wanda aka fi sani da Omolomo, dan asalin Ogwurute Itabono ne a Owukpa. An yi mishi dukan kawo wuka har an kusan kashe shi kafin 'yan banga su kwace shi tare da mika shi hannun 'yan sanda.

An yi wa matashi 'dukan kawo wuka' a kan yi yarinya mai shekaru 7 fyade
An yi wa matashi 'dukan kawo wuka' a kan yi yarinya mai shekaru 7 fyade Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Benue, DSP Catherine Anene, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Trust ta wayar tarho. Ya ce a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun 'yan sanda.

"Zan iya bada tabbacin cewa matashi mai shekaru 26 da aka kama da laifin yi wa yarinya mai shekaru 7 fyade yana hannun mu," Anene yace.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A cikin kwanakin nan ne jama'a a fadin duniya ke ta cece-kuce a kan yawaitar cin zarafin kananan yara da yi wa 'yan mata fyade da ya yawaita.

Wannan ya biyo bayan kisan gillar da aka yi wa Vera Owaila Omozuwa, daliba da ke shekarar farko a jami'ar jihar Edo bayan an yi mata fyade.

An yi mummunar aika-aikar ne a farfajiyar wata babbar coci da ke Benin.

An sake halaka wata daliba mai suna Barakat Bello mai shekaru 18 bayan anyi mata fyade.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel