Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin Gombe, yan majalisa 4, da kwamishana sun kamu da cutar Korona
Kakakin majalisar dokokin jihar Gombe, Abubakar Sadiq Ibrahim, tare da abokan aikinsa yan majalisa hudu sun harbu da cutar Coronavirus, Daily Trust ta ruwaito.
Majiya mai karfi ya bayyana cewa Kakakin tare da yan majalisa hudu, wadanda ba'a bayyana sunayensu ba tukun sun samu sakamakon gwajin da akayi musu kuma ta tabbata sun kamu da cutar.
A cewar majiyar, an killace kakakin da yan majalisan a cibiyoyin killacewa daban-daban a jihar domin jinyarsu, yayinda aka dauki samfurin iyalansu domin gwaji.

Asali: Twitter
Hakazalika, kwamishanan ruwa na jihar, Yahaya Mijinyawa, ya kamu da cutar ta COVID-19.
Kwamishanan ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.
A makon da ya gabata, gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya umurci dukkan kwamishanoninsa, hadimai na musamman, masu bada shawara, da ma'aikatan gidan gwamnatin jihar su gabatar da kansu don gwajin Coronavirus.
Gwamnan ya bada umurnin ne bayan rasuwar dirakta a ofishin sakataren gwamnatin jihar wanda ya kamu da cutar.
A ranar Alhamis, sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya jagoranci ma'aikatan zuwa wajen gwaji.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng