Bayan ganawa da Buhari, Buratai ya bayyana adadin yan Boko Haramun da aka kashe cikin wata 2

Bayan ganawa da Buhari, Buratai ya bayyana adadin yan Boko Haramun da aka kashe cikin wata 2

- Janar Buratai ya gana da shugaba Buhari kan yakin Boko Haram

- Babban hafsan ya koma jihar Borno da zama har sai an kawar da Boko Haram

- Ya ce dakarun Sojin suna samun gagaruman nasarori kan yan ta'addan kuma ba zasu yi kasa a gwiwa ba

Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa dakarun sojin dake Arewa maso gabas sun hallaka yan Boko Haram 1,429 cikin watanni biyun da suka gabata.

Hakazalika an damke masu kaiwa yan ta'addan rahotannin leken asiri 166.

Buratai ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari ranar Litinin 8 ga watan Yuni, 2020 inda ya ce ana samun gagarumin nasara wajen kawar da yan ta'addan.

Babban hasfan Sojin ya bayyana cewa yana kyautata zaton za a cigaba da samin cigaba wajen yaki da yan ta'addan.

KU KARANTA: Kotu ta dakatad da jam'iyyar APC daga gudanar da zaben fiddan dan takarar gwamnan Edo

Bayan ganawa da Buhari, Buratai ya bayyana adadin yan Boko Haramun da aka kashe cikin wata 2
Buhari da Buratai Hoto daga Bashir ahmad
Asali: Twitter

Yace: "Dakarun Sojin na iyakan kokarinsu kuma hakan na haifar 'da mai ido saboda irin nasarorin da muke samu."

"Har yanzu ana gabza yaki kuma an hallaka sama da yan Boko Haram 1,429 kuma mun damke yan leken asiri, jagorori, masu kai musu kaya 166 a cikin kauyuka da dazuka."

"Saboda haka, wannan babban nasara ne, jami'an leken asirinmu tare da jami'an DSS da kuma abokanmu na kwarai yan sa kai CJTF, sun nuna bajinta domin ganin an samu wannan nasaran."

"Ina tabbatar muku da cewa abubuwa za su cigaba da kyau cikin yan kwanakinnan."

Buratai ya ce hukumar bata mayar da hankalinta Arewa maso gabas ba kadai amma har da sauran sassan kasar dake fuskantar barazanan tsaro.

Yace: "Zamu cigaba da kawar da yan tadda zaune tsaye, ba a Arewa maso gabas ba kadai amma dukkan sassan kasa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

kalli biiyon..

Asali: Legit.ng

Online view pixel