Buratai ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Buratai ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Babban hafsan rundonin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa da ke Asorock villa a birnin tarayya, Abuja.

A farkon shekarar nan ne Buratai ya sanar da komawarsa jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram.

A cikin wata sanarwa da Buhari Sallau, hadimin shugaban kasa, ya fitar, ya ce Buratai ya ziyarci Buhari ne domin gabatar masa da jawabi a kan sha'anin tsaro, musamman wadanda suka shafi rundunar soji.

Buratai ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)
Buratai ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Buratai ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)
Buratai a fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Buratai ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)
Buratai ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Batun sha'anin tsaro na kara tabarbarewa a wasu sassan Najeriya, musamman a yankin arewa.

A yayin da mayakan kungiyar Boko Haram ke cigaba da kai hare - hare a sassan jihar Borno, 'yan bindiga da barayin shanu da masu garkuwa da mutane sun hana sassan jihohin Katsina, Sokoto da Zamafara zama lafiya.

A ranar Asabar ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gargadi 'yan bindiga a kan su ajiye makamansu, su mika wuya, ko kuma su fuskanci tozarta da kisan kiyashi.

Sai dai, jama'a da dama sun soki kalaman shugaba Buhari tare da bayyana rashin jin dadinsu a kan gargadin da ya ke yi wa 'yan bindigar da ya zuwa yanzu sun kashe mutane fiye da 8,000.

A kwanakin baya ne shugaba Buhari ya bawa rundunonin tsaro na kasa umarnin su gaggauta kawo karshen 'yan bindigar da su ka addabi jihohin yankin arewa maso yamma, musamman jihohin Katsina, Sokoto da Zamafara.

DUBA WANNAN: Biyan bashi: Buhari ya amince a rabawa wasu jihohi biyar biliyan N148

Rundunar sojojin Najeriya a karkashin atisayen 'ACCORD' da aka kaddamar a jihar Katsina ta sanar da cewa ta samu nasarar kashe wasu 'yan bindiga da barayin shanu a sassan jihar Zamfara a kokarin da ta ke yi na kawo karshen aiyukan ta'addanci a yankin.

A sanarwar da rundunar soji ta fitar ranar Lahadi a shafinta na Tuwita, ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke wani mai safarar makamai ga 'yan bindiga.

Daga cikin kayan da aka samu a wurinsa akwai carbi 496 na alburusai samfurin 7.62mm da babur samfurin 'Bajaj' guda daya.

An kama shi ne a Mararrabar Maigora a yankin karamar hukumar Faskari yayin wani atisaye da rudunar soji ta fita ranar Juma'a, 05 ga watan Yuni, 2020.

A cewar sanarwar, dakarun soji sun sake kashe wasu 'yan bindiga 3 tare da kama wasu 4 yayin wani samame da farautar 'yan bindigar da suka fita ranar Asabar, 06 ga wata, a kauyukan Yauyau da Zandam.

An samu bindigun baushe guda 7, wayoyin hannu guda uku da babura guda biyu a wurin 'yan bindigar.

Rundunar soji ta ce za ta damka 'yan bindigar da ta kama a hannun rundunar 'yan sanda da zarar ta kammala yi musu tambayoyi.

Dakarun sojoji sun kara fafata musayar wuta da wasu 'yan bindiga a kan hanyar Dunya zuwa Dangeza. 'Yan bindigar sun gudu sun bar baburansu guda hudu tare da zubar da bindigunsu guda biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel