Wallahi albashina bai wuce mun kwana 10 yake karewa – Gudaji Kazaure

Wallahi albashina bai wuce mun kwana 10 yake karewa – Gudaji Kazaure

- Dan majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana cewa baya ga albashinsa da alawus babu wani kudi da yake samu daga majalisa

- Gudaji ya kuma tabbatar da cewar albashin nasa basa wuce masa kwana 10 saboda yawan mutanen da yake taimaka wa

- Har ila yau ya jadadda cewa a hakan wasu ma basu san yana yi ba saboda abubuwan basa isa ko kadan kuma kananan hukumomi hudu ke karkashinsa

Honorabul Gudaji Kazaure ya yi magana a kan hanyar da yake bi da kudinsa da yake samu a majalisar wakilai ta tarayyar kasar.

Gudaji ya jadadda cewa baya ga alawus da albashinsa babu wani kudi na daban da ake bashi a matsayinsa na dan majalisa.

Ya kuma bayyana cewa albashinsa kwata-kwata baya wuce masa kwana goma, domin a cewarsa yana karar da kudin ne wajen taimaka wa al’ummarsa. Ya ce duk wata a kalla ya kan taimaka wa mutum 200 zuwa 300.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da sashin Hausa na BBC, inda yake cewa: “Ina tabbatar maka banda alawus dina da salarina babu abunda ake bani.

"A cikinsa nake rike mutane, a cikinsa duk watan duniya a kalla ban taimaka wa mutane ba zan taimaka wa mutum 200 zuwa 300.

“Duk watan duniya tun daga ran da aka zabe ni zuwa yanzu babu ran da albashina zai wuce mun kwana 10. Dukka kudin da ake magana wallahi basa wuce mun kwana 10 saboda an riga idan ka duba yanayin kasar abubuwa basa isa."

Ga bidiyon hirar nasa a kasa:

A gefe guda mun ji cewa Gudaji Kazaure ya bayyana dalilin da ya sa ba zai rika amfani da harshen Hausa wajen magana a gaban majalisa, ganin yadda wasu su kan yi masa dariya ba.

‘Dan majalisar ya ce ya kan yi amfani da Ingilishin ne domin idan ya yi magana ko Bature ne ya ji, zai iya gane inda ya dosa.

Gudaji ya ce hakazalika shi ma idan Bature ya yi masa Ingilishi, zai gane duk abin da ya ke nufi, don haka ya ce babu dalilin da zai ki magana da wannan yare da ya iya sa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel