Dokar kulle: Gwamnatin jihar Kano ta rufe manyan Otal guda biyu

Dokar kulle: Gwamnatin jihar Kano ta rufe manyan Otal guda biyu

Wata kotun tafi da gidanka da ke karkashin mai sharia'a, majistare Aminu Gabari, ta bayar da umarnin rufe wasu manyan Otals guda biyu da ke birinin Kano.

Gabari ya bayar da umarnin rufe manyan Otals guda biyu na tsawon wata shidda bayan samunsu da laifin karya dokar kulle da aka saka a jihar Kano sakamakon bullar annobar korona.

Manayan Otals din da kotun mai lamba ta biyar ta rufe a karshen makon nan sune kamar haka; Mozida Otel da ke yankin No-Man's Land da Otal din Royal Tropicana da ke kan titin Zungeru a unguwar Sabon Gari.

Jami'an tsaron hadin gwuiwa da ke aikin tabbatar da biyayya ga dokar kulle sun kai samame Otals din a daren ranar Juma'a, inda suka kama dumbin mutanen da suka gani suna harkokinsu a harabar Otal din.

A ranar Asabar rundunar 'yan sanda ta gurfanar da kusan mutane 50 da aka kama a gaban kotun tafi da gidanka bisa tuhumarsu da laifin karya dokar zaman gida da gwamnatin jihar Kano ta saka.

Dokar kulle: Gwamnatin jihar Kano ta rufe manyan Otal guda biyu
Dokar kulle: Gwamnatin jihar Kano ta rufe manyan Otal guda biyu
Asali: UGC

Kotun ta ci kowanne mutum daga cikin mutanen tarar N20,000 tare da saka su aikin share manyan titunan birnin Kano na tsawon wata biyu. Dukkan mutanen sun amsa cewa sun aikata laifin da ake tuhumarsu da aikatawa.

DUBA WANNAN: FG ta bayyana matsayin Buhari a kan makomar 'yan N-Power da aka fara dauka

A wani labarin na Legit.ng da ya shafi jihar Kano, hukumar lura da zirga zirgan ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta kama wata mota makil da maganin kara karfin maza da kudinsa ya kai Naira miliyan 25 a unguwar Sabon Gari.

A sanarwar da ya fitar ranar Asabar, Kakakin KAROTA, Nabilusi Kofar Naisa ya ce an gano kwayar mai suna Arofranil ne sakamakon wasu bayyanan sirri da ya nuna magungunan ba su da lambar sahihanci da hukumar NAFDAC ke bayarwa.

A cewarsa, an kama maganin da ake zargin jabu ne a tashar manyan motoci da ke kan titin New Road a cikin unguwar Sabon.

An kama maganin, wanda ke cike makil a mota, kafin a kai ga raba shi zuwa cikin kasuwannin Kano.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel